Kowa ya duba wacce gudummawa zai bai wa Harkar Musulunci - Shaikh Ibraheem Zakzaky

 


Harka (Islamiyya) addini ne, kuma kowa zai duba ne ya ga wane irin gudummawa zai bayar wajen wannan yunƙurin na tabbatan addini. Sannan kuma kowa zai bayar da gudummawa ne da gwargwadon abin da yake iya bayarwa.” Jagora ya bayar da misali da yadda ake gudanar da abubuwa, yace ba kowa ne zai yi wa’azi ba, zai iya zama mutum daya ne mai yin wa’azi a taro, amma kuma dole sai an samu mai tsara wajen taron, da mai hada na’ura, da mai dafa abinci, da sauran abubuwan da in ba da su ba wa’azin ba zai yiwu ba. 

Yace: “Dukkansu kowanne yana bayar da gudummawa ne da abin da yake iyawa, kuma duk suna da amfani, Iklasi ne ake bukata daga kowa a aikinsa. Ya kuma kara jan hankalin ‘yan uwa, akan su fahimci Harka ba muƙami ba ce, balle idan ya zama an raba wani ɗan uwa da wata mas’uliyya da yake gudanarwa, sai yace zai bar Harkar. 

“In dai mutum na Harkar nan don Allah ne, to ko an wayi gari ba shi ke rike da wata mas’uliyya ko wata amana ba, zai cigaba da Harka ne, ba zai ce ya bar Harkar ba.” Ya jaddada. Har ila yau, Jagora ya bayyana yadda al’adar jarabawa take. Yace: “kuma an dinga jarabawa kenan ba ranar da za a daina. Na gaba kan fi ta baya yawa ne.” 

Sannan ya jaddada kira ga ‘yan uwa akan sake daura damarar cigaba da gwagwarmaya saboda Allah, da fatan cinye jarabawowi masu zuwa.  Da yake bayani dangane da aikin Harisanci, Jagora (H) ya bayyana cewa: 

“Harisanci wani karin aiki ne a Harka da aka ce wasu su yi, ba ‘profession’ ba ne, ‘volunteer’ ne, in ka yarda ka yi ne sai ka yi. Ba kuma shi akan kansa ne Harkar ba, ɓangare ne na bayar da gudummawa ga Harka ta wani janibi.” Jagora ya kuma bayyana yadda mahukunta ke kallon Harka a matsayin wata barazana. Yace, mafi yawan jami’an tsaron da ke aiki a yanzu haka, an fara wannan Harkar tun kafin a haife su, wasu kuma tun suna kananan yara, shekara sama da 45 bata taba zama barazana ba, sai yanzu ɗan shekara talatin da wani abu za ka ji ya fito yana ƙoƙarin nuna kamar Harka wata haɗari ce kuma za su magance ta.  

Ya bayyana yadda suke cewa sun yi kutse a cikin Harisanci, inda yace: “Ita Harkar Musulunci buɗaddiyar abu ce, a baya da muke tarurruka a Husainiyyah har soja ko ɗansanda da 'uniform' dinsa sukan iya zuwa su shiga Husainiyyah su ji karatu in sun taso aiki, ba ana hana su ba ne.” Ya kara da cewa: “In kun saka mutanenku a Harisanci, ko ma a wani bangaren Harka, ba yana nufin kun kutsa ba ne, tunda dama budadden abu ne.”

— Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin karɓar rahoton Kwamitin sake nazarin aikin Harisanci, a ranar 14/9/2024. 

Post a Comment

Previous Post Next Post