A yayin ganawarsa ta baya-bayan nan da dubban mata, Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam Sayyid Ali Khamenei, ya sake jaddada cewa wayewar Yammacin duniya na aiwatar da manufofinta kan mata ne ta hanyar yaudara, rashin gaskiya da amfani da taken ’yanci don rufe munanan manufofi.
Imam Khamenei ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da tsarin jari-hujja na Yamma ke fuskanta shi ne aikata wasu munanan dabi’u da yin ikirarin cewa ’yantar da jama’a ake yi, alhali kuwa a zahiri ana ƙara daure su ne cikin tsarin da ke cin zarafi da sarrafa rayuwarsu.
A cikin nazarin da masana daban-daban suka yi, an bayyana hanyoyin da jari-hujja ta Yamma ke amfani da su wajen tasiri ga mata a sassa daban-daban na duniya. Daya daga cikin nazarin ya tattauna ƙoƙarin da ake yi a Amurka da sauran ƙasashen Yamma wajen ƙara yawan shan sigari da barasa a tsakanin mata, duk a ƙarƙashin fakewar ’yancin mata da ’yancin yanke shawara.
A nahiyar Afirka, wasu rahotanni sun bayyana yadda ƙasashen Yamma ke amfani da taken haƙƙin mata da haƙƙin ɗan adam wajen lalata tsarin iyali da al’adun Afirka, lamarin da ake kallon yana haifar da mummunan tasiri kan makomar al’adu da zamantakewar yankin.
Mai bincike kan al’amuran al’adu, Zahra Shafei, ta yi rubuce-rubuce da dama da ke bayani kan yadda tarihi ya nuna amfani da taken ’yancin mata wajen ciyar da manufofin siyasa da kawo sabuwar irin mulkin mallaka, musamman ta hanyar mamaye albarkatun ƙasashe da kasuwanni.
A wani bincike da ta yi a Kudu maso Gabashin Asiya, Shafei ta bayyana rawar da Amurka ta taka wajen bunƙasa masana’antar karuwanci da fataucin mutane, lamarin da ya shafi mata da yara mata da dama a yankin.
Rahotanni daga Hollywood kuma sun bayyana yadda ake amfani da hoton matan Latin Amurka wajen tallafa wa manufofin siyasa da tattalin arziki na Amurka, ta hanyar rarrabe su da siffofi da ba su dace ba.
Haka kuma an yi nazari kan yadda al’adu da dabi’un Yammacin duniya suka shiga kasashen Gabashin Asiya, musamman wajen tasiri ga halayen mata, salon rayuwa da tsarin iyali, a ƙarƙashin manufar bunƙasa jari-hujja.
Wani rahoto ya yi bayani kan yadda ake lalata tufafi da kayayyakin al’adu da suka shafi ƙananan ’yan mata a ƙasashen Yamma don ƙara samun riba, abin da masana suka kira “sayar da rashin kunya” a cikin tsarin kasuwanci.
A gefe guda kuma, masana’antar kayan kwalliya da kula da jiki ta zama babbar hanyar samun riba, inda kamfanoni masu ƙima ke amfani da taken haƙƙin mata da ’yancinsu domin ƙara yawan tallace-tallace, a cewar binciken Zahra Shafei.
Imam Khamenei ya yi gargadin cewa irin waɗannan misalai sun isa su nuna cewa Yamma ba gaskiya take nunawa ba game da ’yancin mata, domin manufarta ita ce samun riba, sarrafa al’umma da kuma wargaza tsarin zamantakewar da ba ya dace da tsarin jari-hujja.
Ya jaddada cewa ya zama dole kasashe su wayi gari a kan wannan tsarin, su kuma kare martabar mata da iyalansu ba ta hanyar bin sawun Yamma ba, sai ta hanyar tabbatar da ’yanci na gaskiya da mutunci a cikin al’adunsu da darajojinsu.

Post a Comment