Cikin alhini da juyayin rabuwar da masoyi, ma'abocin ilimi da imani, ma'abota ilimi da imani sun taru a Karbala mai alfarma, domin nuna alhini ga tsarkakakken jikin marigayi kuma babban Malami kuma ginshiki wajen tsayawa tsayin daka a fannin yada ilimi wato, Ayatullah Sayyid Ali al-Musawi al-Baaj (Allah Ya jikansa), wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ilimi da mujahada da kaskantar da kai, kuma ya kasance daya daga cikin malaman makarantar Hauza kuma ginshiki ta wajen yada ilimin Ahlul-baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su.
Cike da alhini da juyayi aka gudanar da jana'iza ga wannan Babban Malami a dandalin Al-Hussain. A yayin da dimbin muminai suka taru a wurin wanda ya hada da Malamai da dalibai daga bangarori daban-daban inda suka bi sahu. An gudanar da sallar jana'izar wannan Malami ne da Jagoran Shehin Malami Husaini Sheik Abdul Mahdi Al-Karbalai.
Wannan gagarumin jana'aizar ya samu halartar malamai da dama, inda suka nuna alhininsu da bakin ciki kan wannan babban rashi na wannan jarumi a fannin ilimi wanda yake indararo ne na hikima wanda ya bar gadon ilimi da tunani da karamcin da zai dawwama a dalibansa da kuma zukatan masoyansa. Kamar yadda rayuwar Malam Al-Baaj ta kasance mai daraja da ambaton Allah da hidimar addini, tafiyarsa ta kasance abin bankwana mai cike da girmamawa a gare shi, rayuka suka kaskantar da kawukansu, suna tuno doguwar tafiyarsa, a yayin da ya kwashe rayuwarsa mai daraja yana isar da sakon musulunci na kwarai a matsayin jagora da shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici. "Ga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma”
Post a Comment