Khatmar Shaheed Ahmad Week: Daga Zone ɗin Ammar Bin Yaseer



A ranar Asabar 15/11/2025, Zone ɗin Ammar Bin Yaseer suka gudanar da khatma na makon Shaheed Ahmad Zakzaky (H). An fara taron da misalin ƙarfe 12:30 pm, inda aka buɗe taron da addu’a tare da karatun Al-Qur’ani mai girma. Bayan haka aka gabatar da jawabin maraba da baki.

Firkatu Shaheed Humaid (JAFSH) ne suka gabatar da display, sannan mawakan Firkatul Wulaya suka ci gaba da gudanar da nasu waƙen.

An shiga taron kai tsaye tare da gabatar da Malam Ibrahim Tahir, wanda ya yi jawabi akan maudu’i mai taken: “Gwamnatin Musulunci da shibuhohi akan yiwuwar kafa ta a Al'ummar mu.” Bayan kammala jawabinsa, sai Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky suka gabatar da kasaitaccen fareti da display na girmamawa ga Shaheed Ahmad.

Taron ya cigaba da gudana, an shiga zango na biyu ne da bayan gabatar da sallar Zuhraini. Mai jawabi na biyu, Sheikh Isma’il Yusha’u Kudan, ya gabatar da nasa maudu’i mai taken: “Gwagwarmayar Musulunci hanyar fita daga danniya da samun ’yanci.” wanda ya dauki lokaci yana tsokaci game da maudui'n.

Bayan ya kammala, sai aka gabatar da mai jawabi na uku, Malam Yahya Sammaru, wanda ya gabatar da jawabi akan maudu’in “Sadaukarwar Shaheed Ahmad Zakzaky da ayyukansa.”

Bayan kammalawa, sai aka ba da kyaututtuka ga waɗanda suka ci gasar waka, da kuma karramawa ga membobin parade and display. Aka yanka alkaki (cake), aka gabatar da anthem, sannan aka rufe taron da addu’a.

Post a Comment

Previous Post Next Post