Daga Mansur Kabiru
A ranar Litinin ne 18/11/2024 aka gudanar da bukin kaddamar da jami'an tsaro na 'Bomo Community Development Association Security'.
Wannan ƙungiya ce na masu samar da tsaro ga al'ummar garin Bomo da kewaye ta bangarorin da dama kamar su rage yawan sace-sace da sauran su.
Bayan gabatar da fareti na wannan jajirtatttun kuma zaratan matasan na wannan gari Bomo ga al'ummar da suka halarci wannan buki. Shugaban wannan ƙungiya na 'Bomo Community Development Association' Liman Bello Yunusa ya gabatar da jawabi akan kafuwan wannan ƙungiya da kuma aiyukan da wannan ƙungiya ta yi inda ya kawo jajircewan da ta yi wajen kawo karshen kesis na mutane akalla guda 100 da kafuwan wannan ƙungiya sannan ya kara da cewa akwai sabbin tsaruka da suke shirin kawo wa wajen kawoma garin Bomo ci gaba da kewaye.
Sannan a karshen jawabin na sa ya yi godiya ga Mai girma Sarkin Bomo Alhaji Muktar Salihu da nuna goyan baya da bada gudunmuwa ga harkan da ya shafi tsaron wannan gari sannan ya nuna jindadinsa ga Alhaji Lawal Jibrin Bomo da wannan kokarin da ya yi wajen tallafawa ma wannan ƙungiya dari bisa dari. Sannan ya ce za su kara daukar jami'ai karo na biyu mutane dari da tara 109.
Sai jawaban Alhaji Lawal Jibrin Bomo inda ya fara da nuna namijin kokari da jajircewan wannan matasan wajen yin aiki yadda ya kamata inda ya yi albishir da cewa za su taimaka dari bisa dari ga wannan ƙungiya na 'Bomo Community Development Association'.


Post a Comment