Masu Nufin Ɓata Sunan Yari, Na Tsoron Irin Tasirin Siyasarsa Ne - Ƙungiyar BRAC


Wata ƙungiyar siyasa mai suna BRAC Coastal Aborigines ta yi zargin cewa sukar da ake yi wa tsohon gwamnan Zamfara kuma sanata, Abdul’aziz Yari, na da alaƙa da tsoron da wasu ke yi kan ƙaruwar tasirinsa a siyasar Arewacin Nijeriya.

Ƙungiyar ta ce goyon bayan da Yari ke bai wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma ƙarfinsa wajen jagorantar tawagar siyasa a Arewa, hakan ne ya jefa wasu abokan hamayya cikin damuwa.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin, Mai Kula da Ƙungiyar na Ƙasa, Doris McDaniels, ta ce sukar da ake yi wacce ta alaƙanta da yaɗa bayanan ɓata suna, ba su da tushe, kuma sun samo asali ne daga takaici daga 'yan hamayyar siyasa.

A cewarta, Yari ya daɗe yana tsayawa kan matsayarsa cewa ya kamata a bai wa Tinubu damar kammala wa’adin mulkin da ’yan Nijeriya suka ba shi, kuma bai sauya wannan matsaya ba duk da matsin lamba daga wasu ɓangarori.

McDaniels ta yi iƙirarin cewa haɗin kan siyasa tsakanin Yari da Tinubu yana ƙara ƙarfi, kuma yana tasiri kan yadda ake lissafin siyasar zaɓe mai zuwa.

Ta kuma yi zargin cewa wasu ’yan siyasa da ba su gamsu da halin da ake ciki ba sun haɗa kai da jam’iyyun adawa saboda tsoron cewa Yari na da ikon jawo kuri’un Arewa don goyon bayan Tinubu.

“Sukar da ake yi wa Sanata Abdul’aziz Yari da kuma neman ɓata masa suna na nuna takaicin abokan hamayya. Matsayarsa a bayyane take kuma ba ta canza ba; yana ganin ya kamata a bai wa Shugaba Tinubu damar kammala wa’adin da ’yan Nijeriya suka ba shi,” in ji ta.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana taƙamaiman abubuwan da ta kira na yaɗa ɓata sunan da ta ambata ba, kuma ba ta bayyana sunayen mutanen ko ƙungiyoyin da ake zargi da aikata hakan ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post