Me Yasa Muke Muzahara Na Nuna Goyon Baya Ga Iran


Dandalin Yaɗa Labarai na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky yana son bayyanawa a sarari manufar gudanar da muzaharar lumana don nuna goyon baya ga al’ummar Iran da sauran al’ummomin da ke fuskantar zalunci a duniya.

Harkar Musulunci na fafutukar ganin an kafa tsarin adalci wanda ke ɗaukar Musulunci a matsayin hanya guda ta tabbatar da adalci da ɗa’a a zamantakewa. Tsawon kusan shekaru hamsin, Harkar Musulunci ta ci gaba da sadaukar da kai wajen koyarwa, wayar da kan jama’a, da kuma gina tunanin al’umma.

A tsawon tarihi, Harkar Musulunci ta kasance mai goyon bayan al’ummomin da ake zalunta a duniya, daga Gabas zuwa Yamma. Harkar Musulunci ta lura cewa manyan ƙasashe na duniya, musamman na Yamma, sun taka muhimmiyar rawa wajen haifar da matsalolin siyasa da suka shafi Musulmi, Afirka, da yawancin ƙasashe masu tasowa. An kuma lura cewa rashin haɗin kai a wasu ƙasashe na taimaka wa muradun manyan ƙasashe masu ƙarfin siyasa da tattalin arziki.

Harkar Musulunci ta bayyana cewa goyon bayanta ga al’ummar Iran ba sabon abu ba ne. Ta dade tana sukar duk wani farmaki da ake kaiwa ƙasashen Musulmi da sauran al’ummomin da ake zalunta a duk lokacin da irin wannan lamari ya faru.

Duk da cewa akwai mabiya da ke da akidar Shi’a a cikin Harkar Musulunci, yana da muhimmanci a bayyana cewa Harkar Musulunci ba ƙungiya ba ce balle ta taƙaita ga wani bangare na fahimtar addini. Harka ce mai faɗin kofofi da ke karɓar mutane daga mabambantan addini da fahimta, wanda suka yi na’am da manufar ta.

A wannan mahanga, Sayyid Ali Khamenei ba kawai ana kallonsa a matsayin shugaba na siyasa ba ne, har ma ana ɗaukarsa a matsayin jagoran addini a fahimtar Shi’a, kamar yadda Paparoma yake matsayin jagoran addini a Cocin Katolika da ma wasu misalan na wasu addinin.

Harkar Musulunci ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci na hadin guiwar Amurka da Isra’ila da suka kai kan Iran. An bayyana irin wannan aiki a matsayin abin ƙi ga duk masu ‘yan adamtaka a fadin duniya, kuma hukumomin ƙasa da ƙasa duk sun soki wannan harin na tsokana, musamman ganin cewa farmaki ga shugabannin addini ko na siyasa ya saba wa ƙa’idojin duniya da kuma ƙa’idar adalcin ɗan adam.

An yi kira ga al’umma su fahimci cewa wannan muzahara ba ta nufin kare kai ba ce, sai dai bayani ne domin gyara fahimta mara kyau tare da tabbatar da matsayar Harkar Musulunci a tarihi game da adawa da zalunci da azzalumai.

Harkar Musulunci ta sake jaddada cewa za ta ci gaba da tsayawa tare da al’ummomin da ake zalunta a duniya. Dangantakarmu da al’ummar Iran ta ginu ne bisa fahimta da akida ba wai kishin kasa ba, kamar yadda wasu ƙungiyoyi ke da alaƙar akida ko ta siyasa da wasu ɓangarorin duniya.

Muna matuƙar Allah-wadai da duk wani hari ga shugaban addini ko na siyasa mai irin wannan matsayi. Muzaharar mu muzahara ce ta lumana wadda aka shirya domin bayyana alhinin mu da korafe-korafenmu da nuna goyon baya ba tare da wani tashin hankali ba.

Sa hannu:

Dandalin Yaɗa Labarai na Harkar Musulunci

3/3/2026

Post a Comment

Previous Post Next Post