Fasto Methuselah Ndoma na Cocin Dipper Life ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi ga Dandalin Matasan Harkar Musulunci ƙarkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) na Imam Mahdi Zone (Abuja da Suleja), wanda suka kai musu ziyarar sada zumunci a yau Alhamis, 25—12—2025, a Cocin Champion Chapel International dake cikin garin Suleja ta jihar Neja.
Pastor Ndoma ya kara da cewa: "Sheikh Ibraheem Zakzaky Jagoranmu ne, a cikin tafiyarsa akwai Kiristoci, kuma a matsayinmu na Kiristoci muke cikin tafiyarsa." Ya cigaba da cewa: "Sheikh Zakzaky yana faɗa ne da zalunci shi ya sa azzalumai suke son ganin bayansa, don haka ba sai ka zama musulmi bane zaka shiga wannan tafiyar."
A yayin kammala jawabinsa, Pastor ya baiyana irin kokarin da almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky ke yi wajen taimakawa da baiwa al'umma kariya a lokaci mabanbanta. A nasa ɓangaren, Pastor Wesley, shugaban Cocin Champion Chapel International, ya baiyana cewa: "wannan ba shi ne zuwan Matasan na farko ba, shekara da suka shude ma an yi irin wannan biki tare da matasan, muna fatan wannan alaƙa dake tsakaninmu za ta ɗore har abada."
Pastor Wesley ya yi wa Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya addua inda yake cewa: "Girma yana ƙara kama Sheikh Zakzaky, ina rokon Allah ya ƙara masa lafiya." Kafin jawabin, Matasan Harkar Musulunci sun baiyana makasudin zuwanssu tare da karanta takarda da ke dauke da cikakken sakon bikin kirsimeti, suka bayar da kyautuka ga hukumar gudanarwa na Cocin.
Imam Mahdi (ATFS) Zone

Post a Comment