Mun ciyar da mutum 20,000 kullum a makokin Ɗahiru Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi

 

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce ta ciyar da mutum kusan 20,000 kullum yayin makokin Sheikh Ɗahiru Bauchi, wanda ya rasu ranar Alhamis.

Kwamashiniyar Walwala da Jinƙai Hajara Yakubu ta faɗa wa BBC cewa Gwamna Bala Mohammed ne ya ba su umarnin ciyar da mutum 10,000 ko 20,000 a kullum tsawon kwana uku na waɗanda suka halarci jana'izar shehin malamin da aka yi a birnin Bauchi.

"Wannan dalilin ya sa muke hanƙoron ciyar da mutum 10,000 da safe, da kuma 10,000 da dare," in ji ta.

"Ya [Lahadi] ne kwana na uku za mu kammala. Muna bayar da wainar masa da burodi da shayi da kuma kunu da safe. Amma saboda jama'a na da yawa, mukan yi abinci a cikin gida kawai, da kuma wurin manyan baƙi.

"Da dare kuma sai mu raba abincin a cikin mazubi - shinkafa ce kawai da ruwa muke rarrabawa wa mutane da dare."

Post a Comment

Previous Post Next Post