Daga nan aka cigaba da ziyara ga iyalan Shuhada, sannan aka gudanar da muzahara domin tunawa da sadaukarwar su. Bayan muzahara, an gudanar fareti na girmamawa ga Shahidai, daga nan sai Malam Ahmad Nuruddeen Shandam ya gabatar da jawabi kan tasirin jinin Shahidan.
A ci gaba da gudanar da makon a ranar Juma’a 21/11/2025, aka fita hawan dutse (Hiking). Bayan dawowa daga hiking, an gudanar da taron Mauludin Sayyida Zainab (AS) wanda Janahu Sayyida Zainab suka jagoranta; a taron an karanta paper presentation tare da zaman tattaunawa, wato symposiuma tsakanin ɓangarorin yan uwa.
Wannan ya kawo ƙarshen gudanar da rana ta farko da ta biyu na makon Shaheed Ahmad a Zone ɗin Wahab Ibn Abdullah.

Post a Comment