Yadda zaman tunawa da shahadar Sayyida Fatima bintu Rasulullah (s a w) ya gudana a yau talata 04/06/1447, a muhalli Hussainiyya Sayyidil ausiya alƙalawa Shinkafi. Wanda wata riwayar tazo da zancen 03- Jimada thani, shekara ta 11AB. Yayin da wakilin ƴan uwa Malam Ƙasim Shehu yay bitar tarihin mazlumiyyar Sayyida (s a).
A wata gaɓar daga cikin jawabin shehin malamin yake cewa "Lokacin da Imam Ali (a s) yake yiwa Sayyida wanka, cen hannun sa ya taɓo awazar Sayyida, Imam yaji lalle a karye awazar ta ke, a daidai lokacin Imam Ali ya miƙe tsaye ya haɗa kansa da bango Ya riƙa rusa kuka da sauti me karfi, yana cewa sun karya ma ta awaza..." Ya Allah !
Daga Sukhainah Muhammad

Post a Comment