A yau Talata, 4 ga watan Jimada Sani, Hijira 1447, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Nuwamba 2025, ’yan uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) da ke Zariya sun gudanar da zaman jaje na tunawa da shahadar Sayyida Fatima Zahra (S). Ɗan uwa Malam Ahmad Maiwada ne ya jagoranci zaman.
Tun da farko, malamin ya taya Manzon Allah (SAW), Imam Ali (AS) da sauran A’imma (AS) jaje na wafatin Sayyada Zahra. Ya karanta ruwayoyi goma sha takwas (18) da suka kawo ranaku daban-daban da ake dangantawa da ranar wafatin Sayyada Zahra. Sai dai bisa rinjaye, mabiya Ahlul Baiti suna raya tsakiyar watan Jimada Ula ko farkon watan Jimada Sani, saboda ruwayoyin da suka fi karfi a wurinsu.
Malam Ahmad ya yi takaitaccen bayani kan yadda Sayyada Zahra ta yi rayuwa mai cike da ƙunci tun daga rasuwar mahaifinta, Manzon Allah (SAW), da irin abubuwan da suka faru da ita har zuwa rashin lafiya da ta yi wanda ya kai ga rasuwarta. Ya ce, “Akwai abubuwa masu raɗaɗi da suka faru da ita, waɗanda da ma ace ba su faru ba.”
Ya ƙara da cewa, “Yawaitar abubuwan da aka ce sun faru da Sayyada ko abin da aka ce an yi mata, yawancin mutane (Ahlus-Sunnah) suna musun su. Amma akwai wasu muhimman tambayoyi da suka wajaba a yi la’akari da su,” inda ya kawo misalai kamar:
-
Me ya sa aka ruwaito cewa Imam Ali tare da mutane kaɗan ne suka yi jana’izar Sayyada kuma cikin dare?
-
Me ya sa, duk da girman matsayin Sayyada Zahra a matsayin ’yar Manzon Allah (SAW), babu wanda ya iya nuna tabbataccen kabarinta?
A ƙarshe, malamin ya tabbatar da cewa majalisin juyayin Sayyada Zahra da sauran A’imma ibada ce da ke kawo kusanci ga Allah. Ya ce taya mutum jaje a lokacin damuwa ko musiba ya fi nuna ƙauna fiye da taya mutum murna a lokacin biki.
Daga ƙarshe ya yi addu’a ta musamman ga Jagora (H) domin samun kariya da lafiya, tare da roƙon tabbatuwar ɗaukaka ga al’umma.
25/11/2025

Post a Comment