Ranar 1ga rabi'ul Auwal ranar zaa chanza tuta daga ta ashura zuwa ta mauludi ranar bayan mun tashi da safe wajen 12:00 na rana zuwa karfe 1:00 aka kiramu daga Hussainiyya akace sojoji sunzo sun tare hanya anata musayan yawo kafin su fara Harbi zuwa can Kuma aka Kara kiranmu akace sun Fara harbi Sai Lokacin Kuma fito muka tafi Hussainiyya to lokacin da muka zo MTD babu hanyar da zaka Mike ka tafi Hussainiyya Sai dai k biyo ta hanyar GRA Sai ka bullo ta Bayan Hussainiyya gate din bayan mun lokacin da muka shigo Hussainiyya dai muka tarar anata shigo da masu harbi (casulties) da kuma wadanda sukai shahada jikinsu duk jini to gaskiya lokacin hankalina ya tashi sosai Wanda alokacin nayi kuka sosai Wanda inaga Tinda aka Fara waki'ar Ko Ince tinda waki'a ta faru Har ta gama ban tinanin nayi irin kukan ba saboda zaka ga mutum ya fita lafiya lau Amma ya dawo babu wani bangaren Jikinsa koya karye Kuma ga jini yana zuba Ko kuma ace yayi shahada to muna wannan yanayin dai munata kabbarori sukuma Suna ta harbi Sai ya zamo yan'uwa sun rabu kashi kashi wasu na gate din tsakiya Wanda ake cema gate din Sahara wasu kuma Suna gaban gate Wanda ake cema gate din baba yunusa sai kuma gate din baya Wanda ake cema gate din open to haka yan'uwa suka karkasu haka dai yan'uwa sukai ta shigowa wadanda suka samu suka shigo ta barauniyar hanya saboda a lokacin gaban Hussainiyya bazai biyuba Kuma ta PZ ma bazai biyu ba Kuma ta MTD ma baxai biyu ba sai ya GRA ne yan'uwa suke samu suna biyowa tanan bamu dade da shigowa ba sai suka fara raba position a filin polo sai ya zamanto sun ragaye filin har sun billo ta daidai hanyar da zaka billo ta Hussainiyya idan ka biyo ta GRA sai yazamana sunyi wa Hussainiyya zobe babu shiga babu fita to sai ya zamana dai anata ma yan'uwa nasihohi anata Kara karfafa masu gwiwa saboda ranar Sayyid (h) zaizo Hussainiyya to su masu decorations sun cigaba da shirinsu suna sa labule kamar dai hankali a kwance duk da kuma ga tashin hankali nan amma bawai a koma gefe a zauna ba aa kowa na aikinsane a gefe daya kuma ga yan'uwa Suna ta salloli wasu kuma suna waje suna kabbarori su kuma sojojin sun saita Komai Nasu sun saka tankar yaki tana kallon Hussainiyya Wanda tazarar dake tsakanin yan'uwa da tankar yakin baida nisa Kuma ga soja akan bindigan kamar Zaifi harbi haka to mukama sai yazamana mun tara duwatsu da yawa haka daga rana zuwa yamma haka zuwa dare dakwai interlock na Hussainiyya Wanda baa riga da ansaka su ba sai yazamana an farfasa su saboda dasu burazu suke anfani wajen mayarwa jahiliyya din to muna cikin wannan yanayin har mukaga yamma tayi to duk a tinaninmu da yamma yayi zasu iya su bar Hussainiyya saboda basu cimma kudirinsu ba saboda yamma tayi to ashe su shirin da sukai daban ba haka yake ba sunanan kwance ga dare yayi to dai sai muka cire ran Zamu fita Hussainiyya saboda babu hanyar da zaa fita Sannan kuma su sunanan basu tafi ba kamar suna jiran a basu command saboda sun shirya Bindigarsu Munanan dai har yazamanto dare yayi dare ya shiru saboda ranar yan Squad sunyi karatu Kuma yawancinsu basu koma gida ba wasu basukai ga komawa gida ba abin ya rutsa dasu to Akwai yara sosai a cikin hussain din da dare yayi Sai aka dafa abinci haka aka rarraba to a lokacin yan'uwa dai hankali ba a kwance yake ba to Amma dai haka aka rinka cii munci abincin ne kamar munacin magani irin dai aci maganin yunwa saboda babu hanyar da xaa fita ko zaa shigo dole Munanan cikine to mutum dai yayi making mind dinshi Cewa babu abinda ya rage illa ka zauna cikin Hussainiyya to shine dai bamu tada hankalinmu ba irin kai firgicin nan irin ga jam'an tsaro sun ragaye wurin Komai zai iya faruwa kilama zasu iya su wurgo mana boom gaba daya mu mutu to irin wannan fargabar gaskiya nii dai banji shi ba a lokacin to zuwa can da daddare mun kwanta muna bacci sai mukaji sun fara magana though kafin su fara magana mun farka mun tashi saboda sun hasko mana fitilla mai haske bansan ko a jikin motar take ba amma yai Kama da hakan wanda idan suka saitota wuri tana iya hasko masu mutanen dake wajen wurin to kuma sisters da brothers Suna warun sai akace su matsa a wajen saboda zai iya yiwuwa idan sun yi wannan haskawan su iya su saito wajen suyi harbi haka su harbo wani abu mai fashewa to Sai ya zamanto idan suka hasko wuri sai a matsa a wurin Kuma hasken Hussainiyya zai iya taimaka suga Inda mutane suke sai aka kashe bulbs din hussainiya ya zamanto babu haske Sai dai Kawai idan zaka haska koda fitila ko da wayanka babu haske a ciki to a lokacin sai suka fara sanawar cewar duk Wanda yake cikin hussainiya babba ko yaro tsohuwa ta fito ta daga hannunta babu abinda zasuyi mata inaga sun maimaita kamar sau uku to badai a kulasu ba kuma baa ce a fita ba to da sukaji haka can sai mukaji sun fara harbi haka anata harbi muna kabbara to a lokacin da yake mu muna tanan gaban hussainiya kenan saboda sun rabama yan'uwa hankaline akwai wasu ta baya ta gate din baya to mukuma munata gaban Hussainiyya though mukanyi zagaye muyi kabbara sai mu koma nacan baya muyi sai mu Kara dawowa nan to haka dai muka rinka yi to a lokacin mun dawo tanan gaba munata kabbara haka duwarwatsun da muka faffasa ma brothers da yamma sai ya zamanto suna wurin to dasu suka rinka anfani su harbo a bisu da duwatsu ana kabbara hardai aka samu basu iya shigo Hussainiyya ba to Ana cikin wannan Halin ni gaskiya har barci nayi gashidai ana cikin tashin hankaline ana wannan harbe harben amma irin dai firgicin kaga Cewa kaga a cikin matsala wacce baka da tabbacin zaka fita Kuma zaa iya kasheka to bandai san sauran yan'uwa ba amma nidai banji haka ba irin tashin hankalin nan ba sai idan ana harbin bindiga sai mu mu bacci mukeyi tin muna kabbara har bacci ya daukeka muna kwance sai aka harba kubbar hussainiya lokacin muna kwance to nidai kawai na tashi na gammu dukkanmu mun tarwatse da yake muna runfar sisters idan an baro na sayyid (h) muna kwance haka to farkawar da xanyine na gammu haka wasu suna hanyar ban bandaki wasu haryan ta Inda malama suke shigo idan zakaje kitchen idan zaka fita Hussainiyya to abinda dai kamar film haka nake gani saboda yadda naga kubbar hussainiya irin kamar an dagata kamar wani wuta ni abinda idona ya gani kenan to abinda sai Wanda ya gani gaskiya shine Kawai xai iya Cewa ga abinda yake saboda duk yadda zakai ma mutum bayani to bakamar Wanda ya gani ba tom Sai dai aka cigaba da kabbara alokacin tom idan suka ci gaba da harbi sai mu koma mu kwanta muna kabbara har bacci ya daukemu anafa harbin bawai ya tsaya bane Kawai dai harbin bindigar ni dai baya razanani saimu kwanta muyita bacci sai an harba abu mai Kara saimu mu farka muyi ta kabbara a haka dai har Allah ya kaimu washe gari da safe to da Asuba Sai muka Fara shirin yin sallah tinda a lokacin yan'uwa an galabaita mussamma brothers saboda sun kwana basuyi bacci ga gajiya to mudai yawancinmu munyi sallah kowa yayi nashi sai nake cewa Bari naje nayi sallah bansani ba ko zanyi shahada banyi sallah ba to sai nayi alwalwa da wadanda muke tare dasu haka to Nidai nasan na iya yin sallah to sai can aka samu brother yayi Kiran sallah da murya mai Kara haka to kamar jira suke ya idar Sai suka Kara bude wuta da karfin harbi Kawai kakeji to a lokacin da suka Fara wannan harbin sai ya zama karfin nasu yafi Wanda sukai jiya da daddare Sai ya zamo sunaso suci karfin yan'uwa to sunzo gate din Sahara haka sunzo Sai su turo da tankar yaki saisu turo to yan'uwa Suna kabbara Suna binsu da duwatsu haka sai a maida gate din haka aka rinka yi to sai suka koma daga baya suka danno tankar yaki din da karfi sai ya bude to a lokacin da GTE din ya bude sai yazama yan'uwa karfin su ya kare Kuma gate din ya fadi sai su shigo irin yadda suka shigo yadda Kasan ana shooting din film kana kallon American film dinnan sojoji na shigowa irin a dudduke Suna harbi haka suka rinka shigo Suna harbi to alokacin Sai abin ya zamamani kamar ana shooting film saboda abinda kamar Anayin shine a film though a lokacin wayauna baikai haka ba sai ya zamana inata ganin abin wani haka to kankace Meye Kawai sai harbi kota Ko ina to ana cikin wannan yanayinne akace da yan'uwa a kwanta saboda yanzu Gashinan dai muna kallonsu sun shigo Hussainiyya ga wasu burazu Suna tsaye Suna harbinsu da kwafa sai mu akace mana a mu kwanta to a lokacin da akace mana mu Kwanta muna tare da sistoci guda uku Akwai Shahida Fatima M Lawal Akwai Kuma batula Muazu mai fata to saini ina tsakiyarsu muna kwance dai muna kallon cikin Hussainiyya mun bama Bayan sisters baya haka to sai can damadai imani Hawa hawane sai Inda imaninka ya tsaya to anan zaka tsaya sai kawai wani tunani yazo Mani kamar na koma baya saboda wajen bayin sisters din Akwai sistoci da yawa a wurin sai nace bari na koma baya saboda Suna harbi to a lokacin ina tsaye haka sai naji Abu kamar ya taba mani fuska haka to saina taba fuskata nidai banji Komai ba sai nace kila harbine ya bugi gini sai ya tallatsomani haka to na juyo haka na baro batula da Fatima na juyo Ina rarrafe haka tinda muna kwance to nidai baro Inda suke ina rarrafe Wanda yasan bayin Hussainiyya bangaren sister zai gane farkon hanyar da zaka bulla Inda zai shigar da kai strength har wajen famfon da ke Wanda yake bayi Wanda zaka shiga sauran bayikan to inayo kwannan ina rarrafe sai naji kamar an bugani da kasa though ina a rarrafene lokacin kamar mutum yasa hannu daga sama irin ya bugaka da kasa Wanda dole ka kwanta to kuma naji shokin a Jikina sai nayi sauri na dafa Inda naji shokin din a bayana daidai a wazata to sainaji dumi Tom sainaji dumi sai na ciro hannuna to sainaga jini to a lokacin Akwai sistoci a wurin sai aka daukeni ta kaini hanyar bayi idan an shanye lungunnan kafin a shiga cikin bayin to Akwai wani corido haka Wanda akwai tsakanin wancen bayin da wancen bayin to a tsakiyar Wurin aka kwantar dani to sai naji Jikina ya canza inajin xafi amma bansan inane ba to sai aka tambayeni inane aka harbeni sainace Masu bansani ba gaskiya to sai batula Tace taga Inda jini ke zuba Wata sister Fatima hussain ta bada dankwalinta aka daure mani Wurin to a lokacin nidai gaskiya bazan iya kiyaye a lokacin ne aka harbeni sau biyu Ko kafin lokacin aka harbeni Allah Kadai ya sani nidai wannan Wanda naji zafin da ya shiga jikina Sai ya fita to daya tashi fitowane ya fito da Naman jikina to wannan fatar da naman da yayine sai ya zamana inajin xafi to kuma Wurin na taba Sai yazama exit din bullet dinne to wani yashuga jikina ya kwanta akan kashin spinal cord Dina kamar irin a tsira allura haka zaka samaka drip yadda ake tsirata akan jijiya ta kwanta to haka bullet din yayi ya shiga saman spinal cord Dina ya kwanta shi bai fasa kashin ba bai kuma fita ba amma gaskiya bansan Yaushe yashiga ba Kuma nii banma jii zafin shi ba nadai fi kiyaye wancen Wanda ya shiga ya fita shine naji zafi so sai aka kulle Mani shi to a lokacin wakia na kara tsanani cikin Hussainiyya yan'uwa sunata kabbara su Kuma jahiliyya sunata harbi sunata kashe yan'uwa to mu da Muke wurin Bayan an kulle Mani Sai aka taho da Shahida Fatima M Lawal an harbeta a Kai har kwakwalwarta ta irin ta fito to a lokacin kamar ta suma ne ko har tayi shahada bamu sani ba to yan'uwa da suka zo da ita Suna kuka haka to a lokacin muna gefe sai naga gama wacce ta fini tinda ita bama ajin muryarta saina koma gefe inata kuka tinda a lokacin Akwai yarinta haka to sai na koma inata kuka to sai sister batula muaazu take cemani baa kuka addua akeyi saina tuna cewar idan mutum zai mutu salati akeyi to saina fara salati to ni kuma banga alamar mutuwa ba banga malaika ba Kuma ni banji Jikina ko kaina yayi wani iri ba dai irin yadda ake gayamana yadda mutuwa take to Akwai sistoci agun to ni Suna ganin ni nawa ya kare shahada zanyi to sai suka tafi suka samu wuri suka fake haka to nidai banji Komai ba to sainace Nima bari na tashi sai na Mike to Akwai a lokacin Akwai burazu biyu haka akwai Abba Samaru Jan kashi to sai Kuma Muhammad magume to muna tare Amma kamar an harbi abba Samaru din a kafa Amma dai yana tafiya to sai suka cemani inzo Muje to su sisters din da Muke tare dasu a lokacin sun shiga bayin dake hannun hagu to sai mu muka shiga bayin dake hannun dama da yake mu barayin da muka shiga bama a gama ginin ba haka baa gama gyaren shi ba to a cikin bayin sai muka shiga guda daya mu uku kenan muna shiga to muna zaune sai su suka tsaya a zaune sai suke tinanin Meye Zasu iya Mani Wanda koda sojojin sunzo bazasu iya cin Mani ba sai suke cemani idan suka cincidani na hau ba matsala bazanji tsoro ba ko bazan fado ba saina cemasu gaskiya bazan iya ba saboda ban taba ba to sai suka shikenan to muna wajen muna jiwo karar harbi anata kabbara tin munajin muryan yan'uwa to Har rauni ya fara shigarsu aka daina kabbara din sai canne zakaji kabbara din to muna cikin wannan yanayin saiga sojojin sunzo nan bayi to sai sukaje bangaren hannun hagu Kuma kunsan nace maku sistocin da dazun Muke tare dasu duk nan suka shiga to a lokacin da Nidai ina saurarensu haka to a lokacin na tashi daga Inda nake zaune saboda Inda nake zaune idan an bude kofar bayi zaa ganmu idan kuma na tsaya ta bayar kofar bayin to Wanda ya shigo bazai ganni ba irin dan angle din nan dake Bayan koda to sai ya zamanto na dawo wajen na tsaya a tsaye amma inajin jiri haka amma na iya tsayawa a tsayan to sukuma Burazun da muke tare dasu Suna tsaye wajen tailot din to shikenan Sai mukaji sojojin sun shigo to Suna shigowa sai sukayi side din da sisters dinnan suke Suna shiga sainaji Suna cemasu su fito to sai suka fito duk muna Jinsu to Suna fitowa dasu waje to sai suka dawo da inada Muke bangaren bayin da Muke to Suna zuwa Daman Muhammad da abba ne suke tsaye ta wajen to Suna zuwa Sai suka Fara harbi to Nidaman ina Bayan kofane to harbin su ya sama nikuma inata Bayan kofar to a lokacin da suka shigo sukai wannan harbin Daman Muhammad Akwai gwafa a haunnunsa Kuma Yace Indai suka shigo saiya dana masu kwafa to Suna bude kofar sai yayi kabbara ya Kira Sahibul Asr Wazzaman muryar da ban taba jin irin taba Tinda nake kuma ita ba speaker ba Kuma ita ba normal Murya ba muryar da ya Kira Sahibul Asr Wazzaman kenan to yana Kiran Sai ya harba masu kwafa to sai abin ya kona Masu rai damme zai Dana masu kwafa sunma matso kusa dashi Amma shine zaice zai dauki action akai to sai abin ya fusata shi to shi sojan da Muhammad ya danama kwafa yana Kiran Sauran sojoji akan suzo su gani ga wani Civilian ya Dana mashi kwafa irin abin Akwai raini dinnan to sai suka shigo suka janyo Muhammad dashi abba din a kasa jini yana ta zuba amma ni basu iya gani na ba Tom Bayan mintina kadan haka saishi abba suka danne mashi kafar mai harbi din a kasa suka dora Mara harbi a kasa to shine yake cemani Inzo in zauke mashi Sai Muhammad yake Cewa mashi ya kyaleni idan na fito Zasu ganni kuma Zasu kasheni kwara su a kashesu ni na rayu to Ina fitowa lokacin sai ana kiran wayarsa haka to sai ya cemani na kashe wayar to Bayan na dawo Bayan kofar kenan saiga sojojin sun dawo wajen su Muhammad din saboda wannan case din harbin kwafa din da akayi to sunzo Suna Jan abba Sai muhammad ya rike abba Yace babu Inda zasuje dashi sunata dai jainja dashi sai ya zama Indai Zasu ja abba Saidai su jasu dukkansu to sai suka bugama Muhammad interlock a gefen ido to sai kawai y suma to sai kanshi ya kumbura idonshi ya kumbura Shina din sosai to sai jini ya Rufe mashi ido Duk da sunyi tinanun yayi shahada ne Tom sai suka tafi da abba Tom sai suka bar Muhammad a wajen to Lokacin da suka shigo sun ga Shahida Fatima m Lawal Har Suna dubawa ko tayi shahadane inaji Suna fadi Suna Cewa tayi shahaha wasu na Cewa batayi shahada ba to sai suka tafi to ni a lokacin nasan sun sama Hussainiyya wuta da yake Lokacin ana Sanyi to sai yazama Anayin karar wutar to sai nayi tinanin ko wuta Zasu samatane saboda Suna tinanin bata mutu ba to Tinda suka tafi babu sojan da ya kara dawowa Tom Kuma a lokacin anfita da Muhammad to inacikin hakan sai naji ankira ya kira kamar dai sister dinshine ta Kira Tana tambaya ina Mai wayar Sai nake cemata gaskiya yayi shahada Har take tambaya ta ance ansama Hussainiyya wuta to ni Sai nace mata gaskiya ban sani ba saboda ni yanzu ina bayine amma inajin tukukin wuta naci haka to Bayan mun gama wayar Sai nai tinanin na Kira Kawata dake gyallesu to har nayi dialing number dinta saina jibabu kati bashi ne a ciki to saina aje wayar to Ina zaune dai haka shiru shiru Ina tsaye idan na dukuna kofar zai Rufe Kuma idan kofar ya Rufe window ne ke kallon kofar kuma ta window sojoji ke haurawa sunayi wajen kitchen to kuma Akwai yan'uwa Wandada aka harbesu da yawa to Ina tsaye nidai bansan yaya akayi ba Allah shi ya barma kanshi sani amma nayi Bacci mai dadi cikin kwanciyar hankalin ba tare da Wani abuba Tom farkawar da zanyi sai na ganni a zaune duk abin da ya faru da dawo mani to saina firgita to Allah cikin ikonsa Babu sojan da Kara wuce wa ta wurin to sai zama Gani azaune saina Mike na jawo kofar Jikina to sainaji motsi haka to saina ji ana tafiya a hankali to saiya leko ta sakon kofar saimuka hada ido to sai ya cemani kinanan sai nace mashi Inanan Sai naga ciwon nashi fuskarshi ta kumbura idonshi ya bulloku ga kirjinsa an harbeshi to ni sainaji ni bana jin nawa ciwon to saina taba bayana naji inaso na taba inane aka harbeni can sai na taba gurin da nace maku an harbeni ya shiga cikin spinal cord dina ya makale a kashI saina taba nace Ashe nan ya shige kenan to sai Muhammad ya shigo ya bamu wuridi na salatin annabi mukai ta yi nidashi to sai Yace mani gaskiya ya Kamata mu fita mu bar Hussainiyya sai na nuna mashi aa to sai ya bari to sai yanayi yana leko waje wurin da shahhida Fatima M Lawal take to da yana cemani Badai shahada ba tana nurfaffashi haka har ya dawo Yace mani yayi shahada to sai ya kara cemani gaskiya ya Kamata mu bar Hussainiyya sai nace mashi to Tana Ina Zamu bi ga Wanda yasan bayin Hussainiyya bangaren sister bangon dake facing din bayin wannan Sabon gidan da akace sayyid ya siya to sai Yace wannan bangon ya Kamata mu haura mu shiga Dayan ginin to saiyace mani zan iya haurawa Sai nace mashi gaskiya bazan iya ba to saiya cincidani na Kama na hau to a lokacin koda inajin Ciwo idan na kalleshi ga jini ga idonsa to sainaji ni bama Komai bane nawa to Bayan mun hauro saina wani tankin ruwa GP Sai yake cemani ko xamu shiga cikine kinga Ko kwana nawa zamuyi babu Wanda zai ganmu to sainace mashi Aa saboda idan mun shigo yaya zaa mu fito to sai ya cemani Muje ciki Dayake gidan tabako ginine Kala Kala mushiga wannan mu fito haka muka rinkayi to ni Sai nayi give up Kawai nace mashi Kasan Meye Dayake mun shigo mun Cidda Shahidai masu yawa Wanda tinda ga ranar tsoron gawa ya fita Mani a rai saina cemashi Tinda duk nan wajen gawarwakine saina cemashi Kawai mu kwanta acikinsu yadda idan suka shigo sun gammu Zasu dauka munyi shahada to sai yace Mani tom saina samu wani waje na kwanta sai ya samo yayi ya zuba mani to sai shima yaje gefe ya kwanta to wajen dana kwanta akwai Rana Kuma ranar tayi Mani dadi saboda sanyin da ake to sai ga wasu brothers guda biyu da wani yayanmu to sainaji muryarsa dayake inda na kwanta yana kusa da dakin da suka shigane to saina dawo daidai lokacin da Shikuma ya leko da tagar dake dakin sai nake cemashi an harbeni sai Yace maki to ku taso mana sai muka taso sai mukaga Suna tare da sister da wani dan fudiyya to sai Muhammad Yace mu hau Kan bishiya ta yadda idan sun shigo bazasu ganmu bato sai muka hau a lokacin ne mukaga yadda suke dugurguza Hussainiyya to daman yayanmu yaje dubawa idan Akwai hanya to sai ya dawo Yace mani mu sauko sai muka sauko sai muka biyo ta Bayan Hussainiyya muka fito to cikin ikon Allah Sai bamu ga soja ba ko daya tohaka muka fito muka shiga gida baki gidan iyan zazzau Har Mai gadin Yace mana mu shigo sai Muhammad Yace gaskiya Aa bamu da aminci dasu to haka muka bi ta gidan muka haura wata katanga muka sauka muka biyo tacan wajen gidansu su sayyid saboda a lokacin da muka isa GA motar su sayyid Hammad nan dana Sayyida nusaiba da wannan marcedis na sayyid wannan Jan to sai muka shigo har falan gidan mukaga ruwa mukasha Dayake munajin kishi mukasha to sai Muhammad yace mana gaskiya nan ba wurin zama bane saboda nan gurin ma da alamu sunzo sunyi abinda Xasuyi to haka dai muka rinka haura katanga to sai muka haura wani gida muka bulla gidan da su malam tahir yake Bayan mun shiga gidan to gidan Akwai police dog yanata Haushi haka da yake dai Ina tsoron Kare gani a saman katanga na kasa dira to bayan na Dira saing sisters guda biyu da brothers haka da yawa gidanma yayi masu kadan Dayake Mai gidan ya kulle gidan Sai ya bar mana bayi da wani dan korido ana anfani dashi to muna cikin wannan yanayin haka muka Kai cikin dare har ni na gaji Kuma ga raunuka ajikinmu to sai safe mai gadi Yace mai gidan ya bashi keys din gidan muka bude muka shiga to a haka muka rayu Har tsawon kwana uku to duk a lokacin muna waya da yan gyallesu suna fadamana yadda yake ciki to muna haka sai karyar gidan ta haihu shine wani brother yaje ya nemo mata abinci to fitanshi keda wuya sojoji suka biyo shi to sai ya dawo ta gidan shine labulan kofar ya bude sukaga yan'uwa da yawa sai suka ce mana mu fito to su brothers sun fita muma mun fita to Lokacin idan ka fito saisu buga maka sanda to daidai lokacin sai Muhammad magume ya fito Sai suka ganshi sukace ga yaron daya rainasu nan yana jifansu da kwafa to shine dai suka rinka buga mashi karfe Suna dukansa to mukuma Suna mana izgili kalakala Amma basu ce mu cire hijabinmu ba to Bayan sun kashemu a mota sun Kai mu wani depot na yansanda sukace muyi layi Suna mana izgilin wai sunga gumakan da Muke bautawa to bayan sun gama mana hotonan izgilin da suke mana to sai suka kawo abinci suka fara rabawa to a lokacin akwai malam tahir mai kula da Yaran malam to shi sun harbeshi a ciki yana kwance to sai akace duk Wanda aka harbeshi aka waresu waje daban haka suka kwashemu suka kaimu asibitin Shika Wanda acan suka watsar damu to sai yan'uwa suka amshemu suka kaimu emergency aka dubamu daganan gaskiya ban Kara ganin Muhammad ba Bayan kwana biyu sukai mani aiki aka ciro mani bullet to har yanzu dai Akwai buraguzan harsashi a Jikina
Wassalamu Alaikum
Post a Comment