'Yan uwa Fulani Almajiran Sayyid Zakzaky (H) na yankin Zariya sun gudanar da taron Mauludin Nana diyar Usman Danfodiyo a ranar Litinin A Rugan Alhaji Ingel dake Dabai a yankin Zariya. Taron ya qayatar Sosai tunda farko bayan addu'a da mawaqa.
An kuma gabatar da 'yar uwa Malama Sa'adatu Kabir Dabai ta yi jawabi nasihohi ga sistoci don qarfafawa da tsayawa daram wajen Gwagwarmaya da taimaka ma mazaje a gidan da halartat tarukan Harka.
Sai Malam Umar Barte wanda shi ne ya kasance b Baqo mai jawabi ya yi jawabi mai ratsa zukata sosai. Shi Hilanin Rugan ya ce shi fa bai ta6a farin ciki irin wannan ba ganin yadda baqi na kusa dana nesa maza da mata suka cika Rugan gashi kuma Malamai sun yi jawabai sosai.
A hira da muka yi da shi bayan kammala taron ya yi godiya ga Allah da kuma eadanda suka shirya taron ya kuma ce mu isar da saqon gaisuwa ga Jagora Sayyid Zakzaky (H). Wasu Dattawa ma sun yi jawabi a wurin taron inda kowa ya nuna farin cikinsa da wannan taron. Ga wasu daga cikin hotunan taron:
Post a Comment