INNALILLAHI WA’INNAILAIHIR RAJI'UN
Daya daga cikin wanda waqi'ar ya rutsa dashi wato wakilin ‘yan uwa Mal. Muhammad Murtala Yusuf na garin Bomo daga Halqar Ma'asuma Samaru Zaria. Daga ciki ya fara da kawo waqi'ar Daya faru a gabari ana gobe zaa sanya tutar 1 ga watan rabi'ul auwal ranar jumaa Wanda aka samu shahidai Wanda ake halqa masuma tare kamar su Mal. Jibrin da sauran majinyata Wanda aka kaisu asibitin koyarwa ta jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.
A ranar Asabar bayan kammala muzahara a garin samaru Wanda akeyi duk shekara 1 ga wata Kuma ranar ne zaa sanya tutar maulud. Sannan na dauki wakilin yan uwa na samaru Mal. Muhammad Barau samaru, domin duba Yan uwa Wanda aka jinyata a asibiti sannan sai mu koma husainiyya, bayan mu ziyarci Wanda aka jinyata Kuma mu gaishesu sai na fadama Mal. Muhammad zan wuce husainiyya misalin 11:00am na safe.
Bayan na isa husainiyya Kuma Yan uwa sun fara haduwa waje karfe 1:00pm sai mu kaji an fara busa Kaho a kofar husainiyya duk hankalin 'yan uwa ya tashi sakamakon bamu saba Jin irin wannan ba, sai muka fito mu kaga ana hura Kaho sai Kuma motar sojoji ta kawo su gidan Mai ana kofar husainiyya ta aje su da Kuma akwatin harsasai ganin haka Yan uwa ana kazar kazar sai Yan uwa aka tinkaresu Kuma Ina Daya daga cikin su ana tambaya meke tafe dasu suna fadin Babu komai zasu wuce ne kawai, sannan anata tattaunawa dasu haka, Kuma a bisa duk alamu sun zo barna saboda Wanda yazo wuce wa bazai zo da harsasai ba.
Daganan sai musaye waya da yan uwa cewa husainiyya Babu lafiya bayan nan yan uwa suka matsa sai sojojin masa daga sai suka koma filin polo sannan sun aje soja a gurare da dama. Kamar cikin GRA da sauran gurare daga bayan haka ashe sun toshe duk wata hanyar zuwa husainiyya bayan sun koma baya ashe sun je karo karfi ne Kuma Babu shakka sun zo kisa ne, daga sai Yan uwa suka fara ban kwana da salama da Kuma kasan cewa cikin Shirin shahada mun kama hanya zuwa gurin tattaunawa sai mukaji ruwan harbi kawai nan wasu suka kwanta suna harbi suna tahowa duk Wanda suka jikin bishiya haka wandanan fajirai suka fasa Kansu da bindiga innalillahi wa innalillahir raju'un Bayan mun kwanta Muna tafiya nazo shiga husainiyya sai nayi Wani tunanin cewa zasu kewaye husainiyya ne sai na wuce gurin da ake aje mashina sai muka zaga bayan kwatas na rail way Kuma sun riga sun kewaye husainiyya sai dai kabbaran Yan uwa a inda muke tare da wasu Yan uwa suna harbin wasu a Kafa wasu a hannu bayan duhu ya fara sai ga wata tawaga Wanda ake cewa tawagar gwamna ne sukayo ayari da fitullu, Muna nan dai Yan uwa mukayi sallah Amma cikin tashin hankali Kuma dare yayi sannan wasu Yan uwa sunzo daga ba'adin gurare, dare yayi ga Kuma matsanancin sanyi ga Kuma sisters sannan munata tunanin yadda zamuyi Kuma ni a kaina bazan iya dawowa gida ba saboda Koda na dawo Babu abin da zanyi dudda akwaiii daman dawo wa saboda hankali bashi a kwance Sannan kowa na tunanin hadafin su shine ya zasu shima gidan su sayyid daganan sai muka wuce gidan Wani Yan uwa a cikaji muka ci abinci sannan muka cigaba da salloli Kuma muna Jin Abubuwan da suke faru cewa sun isa gudan sayyid sannan sai ga sakon daga jagora cewa a dauki muzahara a kowani sassa na kasar sannan muka fito domin cika umurnin jagora muna tafiya muna kabbara a haka Yan uwa suna fito daga ko Ina muka zagaya gurin karfe 4:00am na asuba sannan muka koma inda muke, da gari ya waye muka tattaunawa da. Sauran Yan uwa cewa zamu shiga gyallesu Muna tafiya mutane na kallon suna mana isgili daga mutanen gari da surutu marasa dadi da yike sun rufe hanyar zuwa gyallesu. Wannan shine iya abinda ya faru damu a waqi'ar Buhari.
Daga Mansur Kabiru

Post a Comment