Dalilin Da Ya Sa Sayyida Jamila Bala Ta Kafa Gidauniyar Garkuwar Sha'iran Birni Da Kewaye


Shugabar Garkuwar Sha’iran Birni da Kewaye Foundation, Sayyida Jamila Bala, ta bayyana dalilan da suka sanya ta kafa gidauniyar, inda ta ce burinta shi ne taimaka wa mata, marayu da sauran masu karamin karfi su samu sana’o’in da za su dogara da kansu da kuma iyalansu.

Sayyida Jamila, wadda aka fi sani da Garkuwar Sha’iran Birni da Kewaye, ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da ta yi da gamayyar ‘yan jarida, ciki har da wakilin FMB PRESS HAUSA, inda ta yi karin haske kan rayuwarta, dalilin kafa gidauniyar, ayyukan da take gudanarwa, nasarorin da aka samu da kuma kalubalen da ke gabanta.

Dalilin Kafa Gidauniyar

Sayyida Jamila ta ce irin ayyukan da take yi a matsayinta na malama kuma ma’aikaciyar jinya, tare da gudanar da sana’ar sayar da magunguna, sun ba ta damar shiga wurare daban-daban da kuma ganin halin rayuwar mata da wasu masu karamin karfi.

Ta ce wannan kwarewa ce ta sa ta fara tunanin yadda za ta taimaka wa mata su samu sana’o’in da za su dogara da kansu, ‘ya’yansu da kuma al’umma baki daya.

A cewarta, rashin sana’a da dogaro da kai na daga cikin matsalolin da wasu mata ke fuskanta, musamman a lokacin da yanayin tattalin arziki ya sa nauyin kula da gida ya kara karfi.

Ta ce burinta shi ne a bai wa mata damar koyon sana’o’in da za su taimaka musu wajen samun abin dogaro da kuma inganta rayuwar iyalansu.

Tallafa Wa Marayu Da Mata

Shugabar gidauniyar ta bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da suka kara karfafa mata gwiwar kafa gidauniyar shi ne yadda ta ga marayu da wasu tsofaffi suna fama da matsalar rashin abin dogaro.

Ta bayar da misalin wasu tsofaffi da ta hadu da su suna bara, inda ta ce bayan tattaunawa da su ta gayyace su zuwa gidauniyar domin su koyi sana’a.

A cewarta, wasu daga cikinsu yanzu sun koyi sana’o’in hannu, ciki har da hada man shafawa, kuma sun daina bara.

Ta ce wasu daga cikin wadanda suka koyi sana’o’in sun fara samar da kayayyaki tare da kai su shaguna domin sayarwa, abin da ta bayyana a matsayin daya daga cikin nasarorin da gidauniyar ta samu.

Mutane 750 Sun Amfana Da Matakin Farko

Sayyida Jamila ta ce tun farko tana da shirin fara horas da mutane 100 ne kawai, amma yawan mutanen da suka nemi shiga shirin ya sanya adadin ya karu zuwa kusan mutum 750.

Ta ce duk da cewa ba ta shirya daukar nauyin mutane masu yawa ba, ta kasa hana wadanda suka zo neman taimako saboda yanayin da suke ciki.

A karshe, ta ce an samu nasarar horas da mutane 750 a matakin farko, inda aka kammala shirin tare da yaye wadanda suka amfana.

Ta kara da cewa gidauniyar ba ta tsaya kan bai wa mutane jari kawai ba, sai dai tana mayar da hankali ne kan koyar da su sana’ar da za su iya amfani da ita wajen dogaro da kansu.

Gidauniyar Ta Fara Ne Da Kudin Da Take Samu Da Kanta

Shugabar gidauniyar ta bayyana cewa a farkon kafa gidauniyar ba ta samu tallafi daga wani bangare ba, inda ta yi amfani da kudaden da take samu daga albashinta da kuma kasuwancinta wajen fara ayyukan gidauniyar.

Ta ce daga baya ta samu wasu gudummawa daga mutane da kungiyoyi, ciki har da ADC, wanda ta ce ya tallafa wa gidauniyar tun kafin fara ayyukanta.

Ta kuma bayyana Alhaji Shu’aibu Mai Canter a matsayin daya daga cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ayyukan gidauniyar.

A cewarta, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafa wa wadanda suka kammala koyon sana’a domin su samu damar fara amfani da abin da suka koya.

Haka kuma, ta ce Mai Girma Bola Ige tare da dan uwansa Mai Elsa sun tallafa wa dalibai 20 da suka kammala sakandare ta hanyar samar musu da guraben tallafin karatu domin ci gaba da karatunsu.

Kalubalen Da Gidauniyar Ke Fuskanta

Duk da nasarorin da gidauniyar ta samu, Sayyida Jamila ta ce rashin isasshen tallafi na daga cikin manyan kalubalen da suke fuskanta.

Ta ce bayan kammala horas da mutane 750, mutane da dama sun ci gaba da zuwa suna neman damar koyon sana’a, amma karfinta bai isa ta ci gaba da daukar nauyin dukkan wadanda suke bukatar shiga shirin ba.

Ta ce saboda haka aka sanya kudin fom naira 1,000 ga wanda yake son shiga, yayin da gidauniyar ke samar da kayan da ake bukata wajen koyar da sana’o’in.

Sai dai ta ce akwai mutane da dama da suke son shiga amma ba su da damar biyan wannan kudin.

A cewarta, a halin yanzu akwai kimanin mutane 200 da suke cikin shirin, yayin da wasu kusan 350 ke jiran damar shiga saboda rashin kudin fom.

Ta ce wani mai suna Alhaji Halliru Dan Amadu ya tallafa wa marayu ta hanyar sayen fom 100 domin su samu damar shiga shirin.

Kira Ga Masu Ruwa Da Tsaki

Sayyida Jamila ta yi kira ga gwamnati, sarakuna, masu hannu da shuni da sauran masu ruwa da tsaki da su duba irin ayyukan da gidauniyar ke gudanarwa tare da tallafa mata.

Ta ce yawancin wadanda ke cin gajiyar ayyukan gidauniyar marayu ne da kuma iyaye mata da ke cikin gidaje.

Ta bayyana cewa karin tallafi zai ba gidauniyar damar fadada ayyukanta da kuma bai wa karin mutane damar koyon sana’o’in da za su taimaka musu wajen dogaro da kansu.

Sayyida Jamila Da Lakabin “Sha’ira”

Da take bayani kan lakabin Sha’ira da ake kiranta da shi, Sayyida Jamila ta ce tana yabon Annabi Muhammad (S), kuma wannan ne dalilin da ya sa ake kiranta da Sha’ira.

Ta ce tana da wasu kasidu da suka shahara a wajen jama’a, musamman wata kasida da ta ce mutane suka fi danganta ta da ita, wadda ake kira “Ranar Tsayuwa”.

Ta ce a lokuta da dama idan aka gayyace ta zuwa majalisu, mutane kan nemi ta gabatar da wannan kasida.

Gaba daya, Sayyida Jamila ta bayyana cewa manufar Garkuwar Sha’iran Birni da Kewaye Foundation ita ce samar da damar koyon sana’a ga wadanda ke bukatar tallafi, musamman mata da marayu, domin su samu damar dogaro da kansu da kuma inganta rayuwarsu.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post