Daga Baqir Nababa
Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta bukaci jin bahasin Aliyu Muhammad (Babagana) wanda a ke zargin Shugaban Karamar Hukuma Kabo da hannu a kama shi kan dalilan siyasa
A yau Talata 22 ga watan Satumba da misalin karfe 9 na safe Aliyu Muhammad wanda ake fi sani da Babagana zai halarci ofishin Rundunar Yan Sandan jihar Kano domin su ji gaskiyar lamarin da kuma bin hakkinsa a kan tsare shi da ake zargin Shugaban Karamar Hukuma Kabo ya sa a ka yi a kan dalilan siyasa wanda a sanaditar haka ya rasa damar rubuta jarabawa.
An bayyana hakan ne cikin wata takardar Æ™orafi mai É—auke da kwanan wata 10 ga Agusta, 2026, wadda aka miÆ™a wa Sufeto-Janar na Rundunar ’Yan Sandan Najeriya a Hedikwatar ’Yansanda da ke Louis Edet House, Abuja.
Takardar ta Æ™unshi Æ™orafi kan kamawa da tsarewa ba bisa ka’idar doka ba, da kuma zargin amfani da ikon ’yan sanda ba daidai ba wajen kama matashin.
A cikin ƙorafin, lauyoyin Aliyu Muhammad Haruna sun bayyana cewa:
“Mu ne lauyoyin Mr. Aliyu Muhammad Haruna (Babagana), kuma bisa umarninsa, mun rubuto wannan wasiÆ™a domin sanar da ku halin da ya dabaibaye kamawa da tsare shi da jami’an ’yan sanda da ke aiki a Sashen ’Yan Sandan Kabo.”
A cewar takardar, lauyoyin sun yi zargin cewa kamawa da tsare Babagana ya faru ne bisa umarni ko sa hannun Shugaban Karamar Hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume Kabo.
LauyoyinLauyoyin sun kuma nemi a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano halaccin kamawa da tsarewar, yanayin da ya kai ga jami’an ’yan sanda É—aukar matakin, da kuma rawar da Shugaban Karamar Hukumar ya taka a cikin lamarin.
Takardar ta bayyana Babagana a matsayin ɗan Najeriya, ɗalibi kuma ɗan asalin Jihar Kano, tare da cewa, bisa bayanan lauyoyinsa, ba shi da wani tarihin aikata laifi da ya shafi wannan ƙorafi.
A ranar 3 ga Mayu, 2026, da misalin Æ™arfe 1:00 na rana, jami’an ’yan sanda da ke aiki a Sashen ’Yansandan Kabo sun je gidan Babagana da ke Gidan Alh. Haruna, Kabo, inda suka kama shi tare da kai shi ofishin ’yan sanda.
A cewar Babagana, jami’an sun É—auki matakin ne bisa umarni ko sa hannun Hon. Lawan Najume Kabo, Shugaban Karamar Hukumar Kabo.
Takardar ta ƙara da cewa Babagana ya taɓa samun rashin jituwa da Shugaban Karamar Hukumar kan wasu batutuwan siyasa da kuma yadda ake gudanar da harkokin ƙaramar hukumar.
Kafin kama shi, Babagana ya kasance yana bayyana ra’ayoyinsa da rashin amincewarsa da wasu manufofi ko matakan gudanarwa da suka shafi Shugaban Karamar Hukumar.
A halin da ake cikin yanzu, lauyoyin matashin suna neman a gudanar da bincike domin tabbatar da ainihin dalilin kamawa da tsare shi da a ka yi, da kuma gano ko an yi amfani da ikon ’yan sanda ba bisa ka’ida ba, a ka ci zarafinsa.
Post a Comment