Matasa Ne Ƙashin Bayan Kowace Harka - Jagora Sheikh Zakzaky (H) a jawabin rufe tadrib na Mu'assatu Abul Fadl Abbas.

 


A ranar Lahadi, 27 ga Satumba 2026, Jagora Sheikh Zakzaky (H) ya rufe Tadrib na kwana biyu da Mu’assasatu Abul Fadl Abbas ta shirya, a gidansa da ke Abuja. A jawabinsa, ya bayyana cewa lokacin samartaka lokaci ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwar mutum. Ya ƙara da cewa, matasa su ne ƙashin bayan kowace gwagwarmaya, ci gabantar da ita da wanzar da ita. 

Ya ce, gina matashi na nufin gina al’umma ne. Jagora ya ja hankali kan makirci da yunƙurin maƙiya na gurbata tarbiyyar matasa, musamman ta hanyar shaye-shaye da shagaltarwa. Ya bayyana muhimmancin fahimtar wannan makirci da yin aiki domin daƙile shi. 

“Na lura an daɗe ana yaƙar mu da wannan, amma kamar mutane ba su fahimta ba. Yana da kyau mutane su fahimci wannan.” A ƙarshe, ya yi kira da neman ilimi da aiki da shi, inda ya bayyana cewa ilimi shi ne jigon ci gaban kowace al’umma. Ya ja hankalin matasa kan guje wa abubuwan da za su shagaltar da su daga abin da zai amfane su, a matsayin wata hanya ta magance waɗannan haɗurran, tare da bayyana muhimmancin aikin ceton matasa da al’umma bakiɗaya daga gare su.

Post a Comment

Previous Post Next Post