Yadda Aka Ƙaddamar da Katafaren Zawiyyar Sheikh Muhajjadina Sani Al-Falaki a Kano

Daga Bello Hamza, Abuja

Al’ummar Musulmi daga Nijar, Ghana, Kamaru, Aljeriya, Maroko da wasu ƙasashe, tare da mutane daga sassa daban-daban na Nijeriya, sun halarci taron ƙaddamar da katafaren Zawiyyar Sheikh Muhajjadina Sani Al-Falaki da aka gudanar a Kano ranar Juma’ar makon da ya gabata.

Taron ya samu halartar manyan malamai, shehunai, muƙaddamai, muridai da sauran al’umma.

Da yake bayani kan tarihin zawiyyar, Sheikh Muhajjadina Sani Al-Falaki ya bayyana cewa gina zawiyyar ya samo asali ne daga gadon da ya samu daga kakanninsa da iyayensa, waɗanda suka taso cikin tafiyar sufaye tare da gudanar da ayyukan ibada a zawiyyoyi. Ya ce akwai zawiyya a gidan kakanninsa da har yanzu take tabbatar da tarihin iyalinsu.

Ya ce wannan tarihi da shawarar magabata, malamai, masoya da almajirai ne suka ƙarfafa shi wajen kafa zawiyyar da za ta zama abin tunawa ga ’ya’ya, jikoki da sauran zuriyarsa.

Sheikh Muhajjadina ya ƙara da cewa burinsa shi ne zawiyyar ta zama cibiyar ibada da ambaton Allah, inda za a gudanar da salloli, wazifa, hailala, istigfari, salatin Annabi da sauran ayyukan ibada da suka dace da koyarwar Musulunci da dokokin ƙasa.

Ya bayyana cewa zawiyyar za ta kasance wajen da al’umma za su iya zuwa domin neman addu’a, shawara, taimako da sauran gudunmawa. Haka kuma, ayyukan gidauniyoyi da sauran hidimomin jin kai da suke gudanarwa za su samu wuri a zawiyyar, ciki har da taimakon masu buƙatar magunguna da wasu abubuwan more rayuwa.

Game da alaƙar zawiyyar da sauran cibiyoyin addini, ya ce tana da kyakkyawar dangantaka da malamai da ƙungiyoyin ibada a Nijeriya da sauran sassan duniya. Ya jaddada cewa zawiyyar ba ta da wata manufa ta tashin hankali ko rikici da wata ƙungiya.

A saƙonsa ga al’umma, Sheikh Muhajjadina ya yi kira da a ƙara tsoron Allah, biyayya, kishin addini, riƙon amana da gaskiya, tare da ƙarfafa soyayya ga Annabi Muhammad (SAW).

Ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, shugabanni na gari, ci gaba da wadata ga Nijeriya, tare da fatan Allah Ya biya wa kowa buƙatunsa na alheri.

Post a Comment

Previous Post Next Post