Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Makarantar Africa Academy, wadda ke gudanar da karatu ta yanar gizo ƙarƙashin Africa TV3, ta gudanar da bikin yaye dalibai 3,500 da suka kammala karatun Diploma a fannin Shari’ar Musulunci.
An gudanar da bikin ne a babban ɗakin taro na sabon wurin Jami’ar Bayero Kano (BUK), inda manyan baƙi daga ƙasar Saudiyya, manyan malamai, shugabannin jami’o’i, ’yan kasuwa da ma’aikata daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.
A yayin bikin, an ba wasu daga cikin ɗaliban da suka nuna hazaƙa tare da samun maki 100 cikin 100 kyautar tikitin zuwa Umara.
Haka kuma, an bai wa wasu ɗalibai takwas da suka biyo bayansu wajen samun sakamako mai kyau kyautar Dala 100 kowannensu.
Manajan Daraktan Africa Media Network kuma Shugaban Africa Academy, Dakta Habib Tijjani Tahir, ya bayyana cewa yaye ɗalibai 3,500 a wannan karo na nuna yadda makarantar ke samun karɓuwa a tsakanin al’umma.
Ya ce a shekarar da ta gabata makarantar ta yaye ɗalibai 2,000, yayin da a wannan shekarar adadin ya haura 3,000, abin da ya ce yana nuna samun gagarumar nasara da kuma fahimtar da jama’a ke yi kan shirin karatun.
Dakta Habib ya ce ana gudanar da karatun ne kyauta, tare da tallafin wasu bayin Allah, domin ba wa jama’a damar samun ilimi ba tare da la’akari da halin da suke ciki ba.
Ya bayyana cewa Africa Media Network na gudanar da wasu shirye-shirye da dama, ciki har da Africa TV3, Afrika Radio, Africa Digital Plus da Africa Academy.
Ya ce tsarin karatun ta yanar gizo ya sauƙaƙa wa mutane samun ilimi, yana mai cewa a yanzu babu wani uzuri da zai hana mutum neman ilimin addini, domin ana iya samun karatun ko mutum yana gida ko wurin aikinsa.
Dakta Habib ya kuma yaba da matakin da shugaban Jami’ar Al-Muhibba ya ɗauka na alƙawarin bai wa ɗaliban da suka yi nasara a jarabawarsu damar ci gaba da karatun digiri.
Ya ce suna fatan sauran jami’o’i za su yi koyi da wannan mataki, domin ba ɗalibai damar ci gaba da karatu da kuma faɗaɗa damar samun ilimi.
A cewarsa, shirye-shiryen kafa Jami’a a ɓangaren Africa Academy sun yi nisa.
Shi ma ɗaya daga cikin iyayen da suka halarci taron, Kwamishina na ɗaya a Hukumar Fansho ta Jihar Kano, Alhaji Hassan Muhammad Aminu, ya bayyana tsarin Africa Academy a matsayin wani shiri mai kyau da ya dace da ƙoƙarin ilimantar da al’umma.
Ya ce ilimantar da mata na da matuƙar muhimmanci, domin idan aka ilimantar da mace, hakan na iya taimaka wa wajen ilimantar da iyali da al’umma baki ɗaya.
Alhaji Hassan ya yaba wa Africa Academy, yana mai fatan Allah ya saka wa masu gudanar da shirin da alheri, tare da kira ga sauran ƙungiyoyi da gidajen talabijin da su yi koyi da irin wannan shiri na tallafa wa ilimi.
Ya kuma yi kira ga masu hali da su taimaka wajen tallafa wa ilimin matasa, musamman ganin yadda halin tattalin arziki ke sanya wasu iyaye kasa ɗaukar nauyin karatun ’ya’yansu.
A cewarsa, taimakon ilimi zai taimaka wajen rage zaman banza da kuma samar da damar da za ta ba matasa damar shiga harkokin da za su amfani kansu da al’umma.
Shi ma ɗaya daga cikin ’yan siyasar da suka halarci taron, Alhaji Musaddik Bashir Tofa, ya bayyana cewa jahilci na daga cikin ƙalubalen da Arewa ke fuskanta.
Ya ce duk lokacin da aka samu wata dama da za ta taimaka wa mutane wajen ƙara ilimi, ya kamata masu son ci gaban al’umma su marabce ta tare da tallafa mata.
Musaddik Bashir Tofa ya ce wannan shi ne karo na biyu da Africa Academy ke gudanar da bikin yaye ɗalibai, inda a karo na farko aka yaye ɗalibai 2,000, yayin da a wannan karon aka yaye sama da 3,000.
Ya ce ƙarin adadin ɗaliban da aka yaye na nuna yadda shirin ke samun karɓuwa, tare da kira ga duk wanda ke da damar tallafa wa ilimi da ya taimaka wajen ƙarfafa irin wannan shiri.
A nasu ɓangaren, ɗaliban da aka yaye daga Africa Academy sun yaba da kulawa da taimakon da malamansu suka ba su a lokacin karatun.
Ɗaliban sun kuma karrama masu gudanar da makarantar ƙarƙashin jagorancin Dakta Habib Tijjani Tahir, bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ganin sun kammala karatunsu.

Post a Comment