Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Ana ci gaba da gudanar da bitar ilimi da horo ga kwararrun masu maganin gargajiya a Jihar Kano, domin basu shaidar kwarewa da za ta basu damar bunkasa harkar magungunan gargajiya daidai da zamani.
Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Kwarewa na Maganin Gargajiya ta Najeriya, Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa, shi ne ya bayyana hakan.
Farfesa Muhammad Ibrahim Jawa, wanda ya assasa makarantar koyar da ilimin maganin gargajiya ta Afirka mai suna MIJ College of Traditional Medicine mai hedkwata a Damaturu kuma ke da rassa a jihohi 25 a Najeriya, ya ce an shirya bitar ne domin tantance masu maganin gargajiya da kuma basu horo na musamman.
Ya ce, gwamnatin tarayya ta amince da tsarin horar da masu maganin gargajiya a karkashin Hukumar Habaka Ilimin Kwarewa na Sana’o’i ta Najeriya , wadda ke karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, kuma tana karkashin Hukumar Kula da Ilimin Fasaha da Kirkira ta Kasa (NBTE).
“An dauki maganin gargajiya a matsayin sana’ar da ke bukatar kwarewa. Mun tsara wani tsari na musamman na ilimantarwa ga masu magungunan gargajiya da gwamnati ta amince da shi. Duk wanda ya ci wannan jarrabawa, za a ba shi shaidar kwarewa,” in ji Farfesan.
Ya bayyana cewa matakan shaidar sun kai daga Mataki na 1 zuwa na 9, inda Mataki na 6 yayi daidai da HND, yayin da Mataki na 9 yayi daidai da digirin digirgir (PhD) da ake bayarwa a jami’a. Wannan horon yana karkashin hurumin hukumar NBTE ne daga Mataki na 1 zuwa na 6.
Farfesa Jawa ya ce, yawancin wadanda ake yi wa bitar kwararru ne da suka dade suna sana’ar, wasu sama da shekaru 50, wasu 30, wasu 25, kuma wasu sun gada ne daga iyaye da kakanni.
Ya ce Gwamnati ta amince da iliminsu da kwarewarsu, amma saboda sun samo shi ta hanyoyi daban-daban, muna son a daidaita su. A samar da fahimtar cuta iri daya, da yaren magana daya, duk da cewa magungunan sun bambanta,” ya ce.
Ya jaddada cewa ba a son a gurbata asalin maganin gargajiya, ko a mayar da shi na bature “Muna son mu dauko maganin gargajiya yadda ake yinsa tun asali yadda ake gane jikin mutum, yadda ake gane cuta da kuma yadda ake hada magani a gargajiyance. Idan muka canza shi, zai gurbata, ba zai zama na bature ba, ba zai zama na gargajiya ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa, wadanda ake yi wa bitar a yanzu suna matakin da za a yi musu jarrabawa a Mataki na 1 da na 2, kuma idan suka samu nasara za a ba su shahada wadda gwamnati ta amince da ita a tsarin daukar aiki na gwamnati (Civil Service Scheme).
“Za a iya daukar ka aiki a gwamnati da shaidarka ta mai maganin gargajiya, ko kuma a baka lasisin bude asibitinka, ko wajen hada magunguna, ko dakin bincike kan maganin gargajiya bisa al’adunmu,” ya bayyana.
A cewarsa, kimanin mutum 60 ne suka yi rajista a rukunin farko na bitar. Daga cikinsu, mutum 10 sun samu horo na musamman kan tabbatar da ingancin sana’a (Quality Assurance) kuma hukuma ta ba su shaidar kula da daidaito da bin ka’idojin sana’ar a Najeriya.
Ya nuna godiyarsa ga gwamnati bisa wannan damar, inda ya ce wannan mataki zai hana zubar da dimbin ilimin da aka tara na shekaru masu yawa.
“Ba daidai ba ne a ce wai rana daya a kore ilimin da kakanni da iyaye suka yi shekaru suna aiki tukuru a kai. Gwamnati ta yi nazari ta ce ba za a kore su ba, sai dai a inganta shi. Su ne ya kamata su jagoranci inganta shi har ‘ya’yansu su zo su koya, domin yawancin kwararrun da ke kauyuka da karkara ne,”

Post a Comment