Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta tarwatsa wata tawagar ‘yan ta’adda a birnin Zahedan da ke kudu maso gabashin Iran, a lardin Sistan da Baluchestan, inda ta kashe mambobin kungiyar shida tare da dakile wani shirin kai harin ta’addanci da suke yi.
Ofishin hulɗa da jama’a na sansanin
Quds na Rundunar Ƙasa ta IRGC ya bayyana a ranar Alhamis cewa an gano tawagar
‘yan ta’addan da sanyin safiya, bayan samun rahotanni daga mazauna yankin da
kuma gudanar da sahihan ayyukan tattara bayanan sirri.
Ya ƙara da cewa mambobin ƙungiyar
suna shirin kai wani harin ta’addanci a yankin.
A yayin samamen, sanarwar ta ce an
kashe mambobi shida na ƙungiyar “‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayin
Takfiri”, yayin da aka gano tare da kwace wasu abubuwan fashewa.
IRGC ta ce har yanzu ana ci gaba da
aikin share maboyar ƙungiyar da ke yankin Manzel-Ab na birnin Zahedan.
Ta ƙara da cewa aikin zai ci gaba da
nufin kawar da sauran ‘yan ta’adda da suka rage a yankin baki ɗaya.
Wannan samame ya zo ne a daidai
lokacin da ake ƙara tsaurara ayyukan yaƙi da ta’addanci a Sistan da
Baluchestan, inda jami’an tsaron Iran suka sha kai samame kan ƙungiyoyin mayaka
da ake zargi da hannu wajen kai hare-hare da kuma ƙoƙarin haifar da rashin
zaman lafiya a lardin kudu maso gabashin ƙasar.
Sistan da Baluchestan, wanda ke da
iyaka da Pakistan, ya fuskanci hare-haren ta’addanci da dama a shekarun baya,
waɗanda suka shafi fararen hula da jami’an tsaro.
Ana zargin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda
da ke kai hare-hare kan muradun Iran da alaƙa da wasu hukumomin leƙen asirin
ƙasashen waje.
An kashe ‘yan ta’adda biyu a yayin gumurzun, yayin da wani guda ya samu rauni sannan jami’an tsaro suka kama shi.

Post a Comment