Harkar Musulunci Ta Kammala Taron Makon Haɗin Kan Musulmi na Mauludin Manzon Allah (SAWW) a Abuja


A ranar Lahadi, 17 ga Rabi’ul Awwal, 1448H, daidai da 30 ga Agusta, 2026, Harkar Musulunci a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta kammala taron Makon Haɗin Kan Musulmi na tsawon kwanaki biyar, wanda aka gudanar domin tattauna rayuwar Manzon Allah (SAWW) da ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’ummar Musulmi a Abuja. 

A farkon taron, an buɗe taron da addu’ar da Shaikh Ahmad Yusuf Yashi ya gabatar. Daga nan Alaramma Aliyu Idris ya karanta ayoyin Alƙur’ani Mai Girma, yayin da tawagar Ittihadu-shu’ara ta gabatar da waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAWW). 

Haka kuma, tawagar IM Production ta gabatar da wasan kwaikwayo na tamsiliyya, inda ta nuna soyayya ga Annabi Muhammad (SAWW), da isar da sahihin saƙo da manufar taron Makon Haɗin Kan Musulmi, tare da bayyana yanayin da Najeriya ke ciki daga mahangar masoyan Manzon Allah (SAWW). 

Hakazalika, tawagar ’Yan Intizar Imam Mahdi (AJTF) ta gabatar da wani shiri na musamman (display). Harkar Musulunci ta fara gudanar da taron Makon Haɗin Kan Musulmi ne a ranar Talata, 12 ga Rabi’ul Awwal, 1448H, daidai da 25 ga Agusta, 2026, a Abuja. 

Taron ya haɗa manyan malamai da masana, daga sassa daban-daban na ƙasar, waɗanda suka gabatar da laccoci kan haɗa kan al’ummar Musulmi da fahimtar juna. A cikin kwanakin da aka gudanar da taron, an gudanar da gasar karatun Alƙur’ani Mai Girma, da kuma faretin girmamawa ga Manzon Allah (SAWW), wanda ɗaliban makarantun Fudiyya suka gabatar. A ranar Lahadi, 17 ga Rabi’ul Awwal, 1448H, daidai da 30 ga Agusta, 2026, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya gabatar da jawabi, ya yanka alkaki, sannan ya rufe taron da addu’a.

©Dandalin Yaɗa Labarai na Harkar Musulunci Ƙarƙashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Post a Comment

Previous Post Next Post