Haɗin Kan Musulmi Shi Zai Dawo Musu Da Izzarsu - Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)


A ranar Lahadi, 17 ga Rabi’ul Awwal 1448, Jagora (H) ya gabatar da jawabin Mauludi tare da rufe taron Makon Haɗin Kai ga ɗimbin mahalarta daga sassa daban-daban na al’ummar Musulmi, a Abuja.

Da yake bayani kan kyawawan ɗabi’un Manzon Rahama (S), Jagora (H) ya ce, “Manzo ya yi galaba ne kan maƙiya da kyawawan ɗabi’unsa,” ta hanyar afuwa, tausayi, rahama da yafiya, har ga waɗanda suka cutar da shi. Ya ce, Manzon Allah (S) ne ya kamata ya zama ramzi da ma’auni ga al'ummar Musulmi.

A ci gaba da jawabinsa, ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin Musulmi, in da ya ce, rauni da koma bayan da Musulmi ke fuskanta na da alaƙa da rarrabuwarsu. Ya yi kira ga Musulmi da su dunƙule su haɗa kai ko don maslahar Musulunci, ya ce hakan ne zai dawo wa Musulmi da izzarsu—abin da maƙiyan Musulunci ba sa so, domin rarrabuwar Musulmi ita ce ke amfanar da su. 

A ƙarshen jawabinsa, ya bayyana cewa, halin da Musulmi ke ciki a yau zai zo ƙarshe, addini zai kafu daram, sannan ƙarfi da izzar al’ummar Musulmi za su dawo, in sha Allah.

@Szakzakyoffice 

Post a Comment

Previous Post Next Post