Daga Awwal Umar Kontagora
A daidai lokacin da Kwamitin Shirya Babban Zaɓen Shugabannin Ƙungiyar Ma’aikatan Ma’adinai ta Najeriya (Nigeria Union of Mines Workers) ke shirye-shiryen gudanar da zaɓen shugabannin ƙungiyar na ƙasa, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 24 ga watan Satumba, 2026, ɗaya daga cikin ’yan takarar kujerar Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Kwamared Musa Adamu Nasko, ya yaba wa Kwamitin Zaɓe na Ƙasa bisa tsarin da ya bi wajen tantance ’yan takarar mukamai daban-daban.
Nasko ya bayyana cewa tsarin tantance ’yan takarar ya kasance na musamman, inda ya ce, a fahimtarsa, irin wannan tsari bai samu ba tun bayan kafa ƙungiyar.
Ya ce tsarin ya bai wa kowane ɗan takara damar bayyana a gaban kwamitin tare da gabatar da manufofinsa da shirye-shiryensa idan ya samu nasarar lashe zaɓe, da kuma hanyoyin da zai bi wajen ciyar da ƙungiyar gaba.
A cewarsa, hakan zai taimaka wajen samar da shugabanci mai inganci da zai iya tabbatar da cewa ƙungiyar ta samu damar yin gogayya da sauran ƙungiyoyin ƙwadago a ƙasar nan.
Nasko ya bayyana haka ne jiya, bayan kammala tantance shi da Kwamitin Zaɓe a Babban Sakatariyar Ƙungiyar.
Ya bayyana gamsuwarsa da tsarin da kwamitin ya bi, yana mai cewa hakan ya ƙara masa kwarin gwiwa cewa za a gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.
A yayin da yake bayani ga wakilinmu, Nasko ya ce tun farko ba shi ne ya nemi tsayawa takarar ba, sai dai ’yan ƙungiyar da yake jagoranta a halin yanzu a Jihar Neja ne suka buƙace shi da ya tsaya takarar.
Ya ce bayan da ’yan ƙungiyar suka biya kuɗin fom ɗin takararsa, bisa jagorancin Sakataren Ƙungiyar, Kwamared Muhammad Ndadzuru Salawu, sun sanar da shi cewa sun kammala nasu ɓangaren na shirye-shiryen, sannan suka buƙace shi da ya fara neman goyon baya da shawarwarin masu ruwa da tsaki a harkar ma’adinai a Jihar Neja da sauran sassan ƙasar.
Nasko ya ce saboda haka ya ga babu wani dalilin da zai sa ya ƙi amincewa da wannan buƙata ta ’yan ƙungiyar.
Ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar ƙungiyar ta samar da ingantaccen tsari na shugabanci da zai bai wa kowa damar bayar da gudunmawa, musamman waɗanda ke fargabar cewa bayan kammala wa’adin shugabancinsu za su rasa wani matsayi ko abin yi.
A cewarsa, idan aka samar da tsarin da ya dace, kowa zai kasance da tabbacin cewa za a ci gaba da tafiya tare da shi ko da bayan kammala wa’adinsa.
Da yake magana kan tambayoyin da kwamitin ya yi masa yayin tantancewar, Nasko ya ce akwai wasu tambayoyi da ba zai iya bayyana wa kafafen yaɗa labarai ba.
Sai dai ya ce tambayoyin da kwamitin ya gabatar masa sun ƙara masa tabbacin cewa ’yan ƙungiyar na da burin ganin ƙungiyar ta samu ci gaba, haɗin kai da ingantaccen shugabanci.
Nasko ya buƙaci masu zaɓe da su ba shi goyon baya tare da zaɓarsa a lokacin gudanar da babban zaɓen, yana mai kira gare su da su yi zaɓe bisa la’akari da cancanta da manufofin ’yan takara.
Ya kuma yi alƙawarin cewa duk wanda bai samu nasara ba a zaɓen, a shirye yake ya yi aiki tare da shi domin tabbatar da cewa kowane mamba ya bayar da tasa gudunmawar wajen ci gaban ƙungiyar, ba tare da nuna bambanci ko wariya ba.
Nasko ya ce ya shafe sama da shekaru 35 zuwa 40 yana aiki a fannin ma’adinai, kuma hakan ya ba shi ƙwarewa da fahimtar ƙalubale da damammakin da ke akwai a ɓangaren.
Ya ce idan aka zaɓe shi, zai mayar da hankali wajen samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga ƙungiyar, ƙirƙiro da dabarun samar da guraben ayyukan yi ga matasa, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar da gwamnati da jami’an tsaro domin dakile matsalolin tsaro da ke addabar wasu yankunan ma’adinai.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta tabbatar da bin dokokin ƙasa da suka shafi harkar ma’adinai, tare da bunƙasa kasuwanci ta hanyar haɗin gwiwa da masu zuba jari, da kuma inganta harkar ma’adinai ta hanyar tabbatar da cewa ana gudanar da ita bisa halastacciyar hanya da dokokin ƙasa suka amince da ita.
Ƙungiyar Ma’aikatan Ma’adinai ta Najeriya na daga cikin ƙungiyoyin ƙwadago da ke wakiltar ma’aikatan da ke aiki a fannin ma’adinai a ƙasar.
A halin yanzu, Kwamared Hamza Mohammed ne ke jagorantar ƙungiyar a matakin ƙasa, yayin da wa’adin shugabancinsa na shekaru huɗu ke gab da kammalawa bisa tanadin dokokin ƙungiyar.
A lokacin mulkinsa, Kwamared Hamza Mohammed ya taka rawa wajen ƙarfafa haɗin kai da ci gaban ma’aikatan ma’adinai, tare da haɗin gwiwar sauran shugabannin ƙungiyar.
Post a Comment