A yammacin ranar Alhamis, 14 ga Rabi’ul Awwal 1448, daidai da 27 ga Agustan 2026, Zawiyyar Marigayi Fadilatu Shaikh Yaqoub Salihu Bomo ta shirya Maulidin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam a zawiyyar da ke garin Bomo.
An soma gudanar da Maulidin ne a yammacin wannan rana, inda Malamai da dama suka gabatar da jawabai har zuwa wayewar garin Juma’a.
Daga cikin Malaman da suka gabatar da jawabai a wajen taron sun haɗa da Shaikh Tafidan Sharifan Zazzau, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli; Limamin Kallan Kura, Imam Umar Sambo; Shaikh Malam Saluhu Khalifa Basawa; Shaikh Malam Salisu Zariya; Shaikh Malam Baba Ahmad Shika, da sauran Malamai.
A yayin jawabansu, Malaman sun karanto tarihin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam, tare da bayyana darajojinsa da martabarsa. Haka kuma, sun yi kira ga al’umma da su yi koyi da kyawawan ɗabi’u da halayen Manzon Allah (S).
Har ila yau, an karanto ruwayoyi da suka nuna ƙima da darajar iyayen Ma’aiki (S), inda aka jaddada cewa kiyaye da kare martabar Manzon Allah addini ne kuma ibada ne.
Malaman sun kuma yi kira musamman ga matasa da su kiyayi Malaman da ke rage ƙima da darajar Manzon Allah da iyayensa.
A yayin taron, Mawaka da Zakirai sun ci gaba da haskaka wajen da ambaton Allah da Manzonsa, lamarin da ya gudana har zuwa wayewar gari.
Post a Comment