FOMWAN Ta Ƙarfafa Tallafa Wa Mata Da ’Yan Mata Ta Hanyar Ilimi Da Sana’o'i

Ƙungiyar Mata Musulmi ta Tarayyar Najeriya, (FOMWAN) ta ƙuduri aniyar ƙarfafa tallafa wa mata da ’yan mata ta hanyar ilimi, kiwon lafiya, sana’o’in dogaro da kai da kuma koyar da dabarun zamani na amfani da fasahar dijital.

An cimma wannan matsaya ne a taron ƙasa karo na 41 na ƙungiyar da aka gudanar a Umuahia, Jihar Abia, wanda ya samu halartar wakilai kusan 600 daga jihohi 36 na ƙasar nan da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).

Taron ya kuma haɗa malaman addinin Musulunci, wakilan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna matsalolin da ke shafar mata, ’yan mata da iyalai a faɗin ƙasar.

A cikin sanarwar da ta fitar a ƙarshen taron, FOMWAN ta nuna damuwa kan ƙaruwa da matsalolin rashin tsaro, talauci, ƙauracewa gidaje, tashin hankali da matsalolin jinƙai, tana mai cewa waɗannan matsaloli na ci gaba da jefa mata da yara cikin halin ƙunci tare da rasa hanyoyin samun abin dogaro.

Ƙungiyar ta kuma bayyana ƙarancin damar samun ilimi ga ’yan mata, kuɗaɗen jari, kasuwanni, kadarorin samar da kuɗi, dabarun fasahar dijital da kuma damarmaki masu ɗorewa na tattalin arziki a matsayin manyan ƙalubalen da ke fuskantar mata da ’yan mata.

Domin magance wasu daga cikin waɗannan ƙalubale, FOMWAN ta kuduri aniyar kafa Shirin Ƙasa na Jagoranci da Taimakon Mata da ’Yan Mata, wanda zai mayar da hankali kan tarbiyya, haɓaka jagoranci, ba da shawarwari kan sana’a, kasuwanci da dabarun rayuwa.

Ƙungiyar ta kuma kuduri aniyar samar da Cibiyar Koyar da Fasahar Dijital, domin bai wa mata da ’yan mata dabarun zamani na fasahar dijital, tare da ƙarfafa shirye-shiryenta a fannonin ilimi, kiwon lafiya, kare yara da kuma ƙarfafa tattalin arziki.

FOMWAN ta kuma yi alƙawarin ƙara wayar da kan jama’a da kuma fafutukar dakile tashin hankali, cin zarafi da nuna wariya ga mata da ’yan mata, tare da ƙarfafa shigarsu cikin ayyukan samar da zaman lafiya, harkokin al’umma da ci gaban ƙasa.

Ƙungiyar ta yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, hukumomin addini da na gargajiya, abokan ci gaban ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki, domin gina mata masu juriya, iyalai masu ƙarfi da al’ummomi masu zaman lafiya.

FOMWAN ta ce irin wannan haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci wajen inganta rayuwar mata da ’yan mata, tare da taimakawa wajen gina Najeriya mai juriya da ci gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post