Daga Fateema Abubakar, Fassarar Ali Kakaki
Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) na ci gaba da bambanta kanta a matsayin ɗaya daga cikin manyan jami’o’in masu zaman kansu a Jihar Kano da yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ƙudurin jami’ar na samar da ingantaccen ilimi, ƙwarewar ilimi, ingantattun kayayyakin more rayuwa, tarbiyya da kuma gina kyawawan ɗabi’u, ya sanya ta zama jami’ar da ɗalibai ke zaɓa domin samun ilimin da ya dace da matakin duniya.
Abin da ya sa MAAUN ta yi fice ba wai kawai kyawu da ingancin gine-ginenta ba ne, har ma da ingancin ilimi da horon da take bai wa ɗalibanta. Jami’ar ta samar da yanayi mai kyau da ke ƙarfafa ɗalibai su koyi abubuwa, su ƙirƙira, su bunƙasa baiwarsu, tare da shirya kansu domin bayar da gudunmawa mai ma’ana ga al’umma.
Nasarorin da ɗaliban MAAUN suke samu sun isa su tabbatar da hakan. A shekarar 2025, wani ɗalibin Sashen Sadarwa da Yaɗa Labarai na jami’ar ya samu karramawa a bikin ‘Campus Journalism Awards’ da aka gudanar a Transcorp Hilton, lamarin da ya nuna ƙarfin horon da jami’ar ke bayarwa a fannonin sadarwa, aikin jarida da rubuce-rubucen ƙirƙira. Haka kuma, ɗaliban Kimiyyar Jinya na MAAUN sun ci gaba da nuna ƙwarewa da kwarewar aiki a lokacin horon aikinsu na asibiti a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a faɗin ƙasar.
Wani babban ƙarfin MAAUN shi ne ma’aikatan koyarwarta. Jami’ar ta haɗa ƙwararrun malamai da masana waɗanda suka himmatu wajen koyarwa, bincike, jagoranci da kuma ci gaban ɗalibai gaba ɗaya. Ƙoƙarinta na tabbatar da gaskiya a harkar ilimi, tarbiyya, daukar mataki kan cin hanci da rashawa da cin zarafi, da kuma girmama mutuncin ɗan Adam, na taimakawa wajen samar da zaman lafiya da kyakkyawan yanayin karatu.
Ni da kaina, na shaida irin martabar da MAAUN ke ginawa a wajen Kano. Duk lokacin da na yi tafiya kuma na ambaci cewa ni ɗaliba ce a MAAUN, sau da yawa mutane kan nuna sha’awa da kuma yabawa jami’ar nan take. Irin wannan karɓuwa ba ta faruwa haka nan kawai; alama ce ta tasirin da jami’ar ke yi.
A MAAUN, ilimi ya wuce samun takardar shaidar digiri kawai. Ana koyar da ɗalibai fannonin da suka zaɓa, yayin da kuma ake ƙarfafa su wajen gina kyawawan ɗabi’u, tarbiyya, girmama malamai da abokan karatu, da kuma fahimtar nauyin da ke kansu ga al’umma. A don haka, jami’ar ba wai kawai suna kokarin samar da waɗanda suka kammala karatu bane, suna samar da masu kyawawan ɗabi’u da amfani ga al’umma.
Ina matuƙar alfahari da ƙara samun karɓuwa da MAAUN ke samu a cikin kimantawar manyan makarantun gaba da sakandare ta ƙasa da ƙasa. MAAUN da American University ta Najeriya (AUN), Yola, suna cikin jami’o’in Najeriya 24 da aka saka cikin jadawalin manyan jami’o’in duniya na ‘Times Higher Education (THE)’ na shekarar 2026. Shigar MAAUN cikin ɗaya daga cikin fitattun tsarin kimanta jami’o’in duniya na nuna yadda jami’ar ke ƙara samun matsayi da kuma shiga cikin harkar ilimi ta duniya.
Jadawalin na shekarar 2026 ya ƙunshi jami’o’in Najeriya 24, waɗanda suka haɗa da jami’o’in gwamnati 17 da jami’o’i masu zaman kansu bakwai. Daga cikin jami’o’in da suka yi fice a Najeriya akwai jami’ar Ibadan, Jami’ar Lagos da Jami’ar Bayero Kano.
Haka kuma, MAAUN ta samu gagarumar karramawa a ‘AD Scientific Index’, wani tsarin kasa da kasa na tantancewa da jera jami’o’i da masu bincike, wanda ke duba jami’o’i da masu bincike bisa la’akari da alamomin yawan binciken kimiyya da tasirin ayyukan ilimi. A cikin ‘AD Scientific Index’ na shekarar 2025, an sanya MAAUN a matsayi na biyu a tsakanin jami’o’in Najeriya, yayin da jami’ar Covenant ke matsayi na farko. Wannan karramawa tana da muhimmiyar ma’ana saboda tana nuna yadda jami’ar ke ƙara bunƙasa a fannin ilimi da bincike, ba wai kawai ta fuskar gine-gine da kayayyakin more rayuwa ba.
Haɗuwar bayyanar MAAUN a cikin jadawalin manyan jami’o’in duniya na ‘Times Higher Education’ na shekarar 2026 da kuma matsayinta na biyu a ‘AD Scientific Index’ na shekarar 2025, na nuna cewa ci gaban jami’ar na ƙara samun karɓuwa ta hanyar tsarin kimanta ilimi da bincike na kasa da kasa. Ga jami’a mai zaman kanta wadda ba ta daɗe da kafuwa ba, irin wannan karramawa babbar nasara ce kuma alama ce ta burin jami’ar na yin gogayya fiye da yanayin da take ciki a yanzu.
A Arewa maso Yamma, MAAUN tana ci gaba da kafa kanta a matsayin muhimmiyar cibiyar ilimi mai zurfi. Kasancewar jami’ar a Kano ya kuma taimaka matuƙa wajen ci gaban al’ummar Hotoro. Jami’ar ta jawo ɗalibai, malamai, ’yan kasuwa, bunƙasar gidaje da sauran harkokin tattalin arziki, wanda ya taimaka wajen sauya fasalin yankin tare da ƙara wa yankin muhimmanci.
Ana cewa jami’o’i suna gina birane, kuma MAAUN misali ne bayyananne na hakan. Tasirinta ya wuce aji da karatu, har ya shiga cikin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Jihar Kano.
A matsayina na ɗaliba a Sashen Kimiyyar Jinya a MAAUN, ina alfaharin kasancewa cikin wata cibiya da ke ci gaba da neman ƙwarewa, samun karɓuwa a cikin jadawalin jami’o’i na ƙasa da ƙasa, da kuma ɗaga matsayin ilimin jami’o’i masu zaman kansu a Kano da Arewa maso Yamma.
Allah Ya ƙara wa MAAUN ɗaukaka!
Allah Ya ƙara wa Jihar Kano ɗaukaka!
Allah Ya ƙara wa wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, lafiya da nasara!
Fateema Abubakar ɗaliba ce a Sashen Kimiyyar Jinya na jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN).
Post a Comment