Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
ya gabatar da jawabin rufewa a yayin taron shekara-shekara karo na 12 na tunawa
da waƙi'ar Ƙudus ta ranar 25 ga watan Yulin 2014. Taron wanda aka saba gudanar
da shi a duk shekara, a Abuja, a bana ya gudana ne a yau Asabar 17 ga Safar,
1448 daidai da 1 ga watan Agustan 2026, tun daga misalin ƙarfe 10 na safe zuwa
yammaci.
Jawabin wanda Jagora (H) ya gabatar
a cikin harshen Ingilishi, ya soma ne da bayyana yadda taron ya kasance na
tunawa da abin da ya faru a ranar Ƙudus shekaru 12 da suka gabata. Jagora (H)
ya bayyana yadda sojoji kwatsam suka zo suka buɗe wuta kan masu muzaharar nuna
goyon baya ga al'ummar Falasɗinu a Zariya, inda ya ce an bizne mutum 31 a muhallin
Darur Rahma, a yayin da 2 daga shahidan aka bizne su a garuruwan su bayan masu
haƙƙi da gangar jikin sun buƙaci haka.
Kazalika Jagora (H) ya bayyana ɗayan
a matsayin Julius Anyanwu wanda Kirista ne kuma Ibo da sojojin suka kashe a
lokacin muzaharar. Jagora ya yi tilawar yadda Harkar Musulunci ta turo wakilai
a yayin bizne shi a jiharsa ta Abia.
Jagora (H) ya yi bayanin yadda aka
soma muzaharar Ƙudus a nan ƙasar tun bayan ayyana Juma'ar ƙarshe ta ranar Ƙudus
wanda Marigayi Imam Khumaini (QS) ya yi. Ya ce, tun a 1980 aka soma Ƙudus a
Nijeriya amma a lokacin ana yi a ɗakin taro a cikin Jami'a har zuwa 1983.
Jagora ya ce daga 1984 aka soma gudanar da muzaharar Ƙudus a wajen Jami'a, inda
ya ce muzaharar da aka afkawa a 2014 ita ce taro kan Ƙudus na 33. Jagora ya yi
bayanin yadda aka kama wasu da ran su a lokacin muzaharar, kuma aka azabtar da
su har aka kashe su.
Da yake ci gaba da bayani, ya
nusasshe da yadda aka gudanar da taro bayan cika kwanaki 40 da waƙi'ar wanda ya
gudana a Darur Rahma, da kuma yadda aka yi taron shekara ɗaya da cikar waƙi'ar
a Zariya da Abuja.
Ya yi ƙarin haske dangane da yadda
aka yi ƙoƙarin maishe da kisan kiyashin da ake yi wa Falasɗinu a matsayin
'rikici ne tsakanin Isra'ila da Falasɗinu' - inda ya ce abubuwa sun canja tun
bayan juyin juya halin Musulunci na Iran a 1979. "Sai ya zama Ƙudus ta
zama al'amari ne na duniya. Yanzu an san shi a matsayin ranar Ƙudus ta
duniya", ya jaddada. Ya kuma lurantar da yadda kafin ƙirƙirar
haramtacciyar ƙasar Isra'ila a 1949, yadda musulmi ke zuwa Ƙudus domin ibada
bayan sun dawo aikin Hajji.
Jagora (H) ya lurantar da cewa
Sahayoniyawa ba Yahudawa bane, mutane ne kawai dake son danniya da mulkar
duniya: "mutane ne masu fifita fata. Suna son mamaye duniya ne". Ya
tabbatar da cewa su ba Kiristoci bane, ko Yahudawa, su Sahayoniyawa ne masu
ra'ayin siyasar mamayar kowa. "Sahayoniyanci ƙirƙirarren ra'ayin siyasa ce
domin mamayar duniya", ya lurantar. Ya yi ƙarin hasken na yadda Imam
Khumaini (Q.S) ya fallasa wannan zalunci da tuggun Sahayoniyawa, da yadda
al'amarin Ƙudus ya tumbatsa a duniya kowa ya runguma tun daga musulmi, kirista
da ma Yahudawa da suke Allah-wadai da Sahayoniyawa.
Jagora ya ƙara da cewa; "mu ba
muna ƙin addini bane, muna ƙin zalunci ne.... Muna goyon bayan raunana a duk
inda suke a duk faɗin duniya ko a Falasɗinu ko a Rohingya ko a ina ne ma".
Ya ce atisayen Ɗufanul Aƙsa ya sake
fallasa ta'addancin Isra'ila kan Falasɗinu inda ya bayyana kamar hasken rana
al'umma suka fahimci irin girman kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa.
Ya ce; "ƙarairayinsu ya fara dusashewa. Yanzu mutane sun fahimci mafi
munin ƴan ta'adda a duniya".
Jagora ya nusasshe da cewa burin
Sahayoniyawa da Sahayoniyanci shi ne kafa abin da suka kira "babbar
Isra'ila", sai dai ya ce babban kulensu ga cimma wannan mafarki shi ne
Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda ya ce shiyasa suka yi ƙoƙarin kawar da ita
a Yunin shekarar da ta gabata wanda a ƙarshe suka nemi sulhu. Ya ce a yanzu ma
sun sake gwadawa domin cimma haka, kuma yanzu wata biyar ke nan amma haƙar su
ba ta cimma ruwa ba. Inda Jagora (H) ya jaddada cewa; "buƙatar su ta kafa
'babbar Isra'ila' mafarki ne da ba zai taɓa haƙƙaƙuwa ba", ya tabbatar.
Ya ce, Amurka ta yi faɗuwar baƙar
tasa a Iran, amma suna ƙi-faɗi ne, sai dai Jagora ya ce, faɗuwar ta su za ta
bayyana kamar hasken rana.
Dangane da al'amarin Ƙudus kuwa,
Jagora ya ce ranar ƙudus ta duniya "ba kawai rana ce ta nuna goyon baya ga
Falasɗinu bane, rana ce ta nuna goyon baya ga raunana a duniya. Rana ce da muke
cewa muna ƙin zalunci a duk inda yake a duniya", ya jaddada. Sai dai ya
nuna takaicinsa na yadda a wannan ƙasar aka raba mutane da sunan addini, ƙabila
da kuma ɓangaranci.
Dangane da masu kisan masu nuna
damuwarsu da lamarin Ƙudus a nan ƙasar kuwa, Jagora (H) ya jefa musu kule, inda
ya ce; "muna ma ku kule, tunda kuna goyon bayansu ido rufe; idan kuna
goyon bayan Isra'ila ba hari ya kamata ku kawo mana ba a lokacin da muka fito
muzaharar nuna goyon baya ga Falasɗinu, ku ware watarana da ba ranar Juma'ar
ƙarshen watan Ramadan ba, ku fito ƙwanku da ƙwarƙwata domin nuna goyon bayanku
ga Isra'ila, kuna da ƴancin ku yi haka, ba za mu ce muku komai ba; amma mene ne
na kashe mu?", ya yi musu kule.
Sannan ya nusashe da cewa;
"Abin da yakamata mu sani cewa, wannan yaƙi (tsakanin Amurka da Iran),
yaƙi ne tsakanin gaskiya da ƙarya, yaƙi ne tsakanin azzalumai da wanda ake
zalunta. Kuma ya kamata ka kasance a kyakkyawan ɓangaren tarihi. Ka zaɓi ɓangaren
da kake so. Kuma mu muna goyon bayan waɗanda ake zalunta ne kan waɗanda suke
zalunci. Kuma za mu ci gaba da yin hakan".
Ya ci gaba da cewa; "za mu fito
tattaki a Abuja da baƙaken kaya domin nuna goyon baya ga Imam Husaini. Da kuma
nuna cewa muna goyon bayan waɗanda ake zalunta kuma muna Allah-wadai da nau'in
kowanne zalunci. Mu kuma ba ma ƙin kowanne addini, ko wasu, ko wani, muna goyon
bayan raunana da ƙin waɗanda suke zalunci. Kuma zalunci ba zai dawwama ba.
Wannan ƙasar ba za ta dawwama a yadda take ba, tabbas za a samu canji, muna
fatan insha Allah, da mu, da ku baki ɗaya za mu kasance wani ɓangare na wannan
canjin".
Tunda fari an soma taron da buɗe shi
da addu'a, karatun Alkur'ani mai girma da jawabai daga Farfesa Abdullahi
Danladi, daga jami'ar ABU, Barista Alzubayr Abubakar, Dr. Shamsuddeen Hassan,
wanda ya yi jawabi a madadin Chief Ebenezer Onyetakin, Bro. Sani Abdu daga
jamhuriyar Nijar, Dr. Qasim Muhammadi sai kuma Omoyele Sowore.
A ƙarshe Jagora (H) ya rufe taron da
addu'a. Sannan aka yi 'exhibition', aka sallami mutane.
@Szakzakyoffice

Post a Comment