Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
ya gabatar da jawabi a taron tunawa da waƙi'ar Ƙudus ta 25 ga watan Yulin 2014.
Taron ya gudana ne a yau Asabar 25/7/2026 a muhallin Darur Rahma da ke Dambo, a
Zariya.
Jagoran ya fara jawabinsa da nuna
alhini dangane da waƙi'ar Ashura da kuma wafatin Imam Hassan Mujtaba (A.S).
Sannan ya tunatar dangane da arba'in da ake fuskanta, da kuma jana'izar
shahidin wannan al'umma, Shahid Sayyid Ali Khamene'i (RH).
Jagora ya jaddada cewa: "wannan
taron, taro ne na tunawa da waƙi'ar da ta auku a ranar 28 ga watan Ramadan,
1436 daidai da 25 ga watan Yulin 2014. Shekaru 12 ke nan cif-cif a ƙidayar
miladiyya."
Har wa yau, Jagora (H) ya tunatar da
yadda aka soma muzaharar Ƙudus a Nijeriya, wadda aka fara gudanar da ita a
Juma'ar farko bayan watan Ramadan a Zariya. Daga bisani kuma ta faɗaɗa zuwa
sassan ƙasar nan sakamakon ƙaruwa da yawan jama'ar da ke halarta. Haka kuma ya
yi bayanin yadda al'amarin Falasɗinu ya samu karɓuwa a tsakanin al'umma.
"Muzaharar Ƙudus na duniya nuna
goyon baya ne ga al'ummar Falasɗinu wanda ƴan share wuri zauna ke musgunawa da
zaluntar su tsawon shekaru fiye da 70", inji Jagora.
Ya ƙara da cewa: "Ana nuna
cewa, ba a yadda da zalunci ba ne."
Har wa yau, a wani ɓangare na
jawabinsa, Jagora ya tunatar da al'umma dangane da waƙi'ar da ta auku a rana
irin ta yau. Ya ce, muzaharar Ƙudus ta wannan shekarar (2014), a nan ƙasar ne
kawai aka auka mata. Ya ce: "wannan abin da ya faru bai ɓoyun ma al'umma
ba. Ashe ba su dandara ba bayan shekara guda suka sake diran mana da nufin
share kowa da kowa. Da ma manufar ke nan a waƙi'ar 25 ga watan Yulin 2014 sai
ya ƙare kan mutum 34", ya nusasshe.
Dangane da masu afkawa muzaharar
Ƙudus domin faranta ran Isra'iliyawa, Jagora (H) ya ce, abu ne mai sauƙi:
"tunda mu muna nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Juma'ar ƙarshen watan
Ramadan, sai ku ware watarana ba Juma'ar ƙarshen watan Ramadan ba sai ku goyi
bayan Isra'iliyawa".
Jagora (H) ya jaddada cewa, ba za a
ba mu tsoro da mutuwa ba: "ko ku yi harbi, ko kar ku yi harbi, za mu
fito". Sannan ya ce, irin wannan taro, taro ne da ake tuna rayayyu da
nassin Alƙur'ani. Ya ƙara da cewa: "idan aka ce an ga shahidi da ido, ba
ma shakka", ya lurantar.
Jagora (H) ya ce, ko an kashe mutum
ko kuma aka bar shi da rai, a ƙarshe dai zai mutu. Ya ce: "Abin alfahari
ne a kashe ka a tafarkin Allah". Jagora ya nanata cewa, muna nan daram a
wannan tafarki da aka kashe waɗannan shahidai. Ya ce: "muna nan daram a
wannan tafarki da kuka bayar da rai a kai, ko a karrama mu, ko mu mutu a kan
wannan tafarki, amma ba za mu sauya ba".
Dangane da masu kisan kai kuwa,
Jagora (H) ya ce, su tuba, amma idan ba su tuba ba, za su yi hasarar duniya da
lahira.
A ƙarshe, Jagora ya jaddada cewa:
"wannan taro namu alama ce ta so, muna son waɗanda suka sadaukar da
rayuwarsu a wannan tafarki. Kuma kowannen mu hanƙoransa ke nan. Muna tunawa da
wannan, muna ganin muna samun lada ne".
Bayan kammala jawabin, Jagora (H) ya
gaisa da malamai, fastoci da sauran baƙin da aka gayyata zuwa taron, tare da
iyalan Shahidai. Daga nan sai ya gudanar da ziyarar ƙaburburan Shahidan da ke
kwance a Darur Rahma, sannan aka sallami al'umma.
Tun da farko, an fara taron da buɗe
shi da addu'a, sannan aka yi karatun Alƙur'ani Mai Girma. Bayan haka aka
gabatar da display daga lajanoni, tare da Faretin girmama Shuhada, sai kuma
tamsiliyya da ta shafi waƙi'ar. Bayan kammala ziyarorin, Jagora (H) ya rufe
taron da addu'a.
@SZakzakyOffice

Post a Comment