NUMW Ta Rantsar da Zababbun Shugabanni 23 na Paikoro

Daga Awwal Umar Kontagora

Ƙungiyar Ma'aikatan Ma'adinai ta Najeriya (Nigeria Union of Mine Workers – NUMW), reshen Jihar Neja, ta rantsar da zababbun shugabanni 23 domin jagorantar reshen ƙungiyar na Ƙaramar Hukumar Paikoro.

An gudanar da bikin rantsuwar ne a sakatariyar ƙungiyar da ke Minna, inda Dagacin Yamman Paiko, Alhaji Abdullahi Bawa, jami'an tsaro, da shugabannin ƙungiyar daga ƙananan hukumomi daban-daban suka halarta. An kuma samu halartar shugaban riƙo na reshen Ƙaramar Hukumar Borgu, Kwamared Habu Idi, tare da sauran shugabannin ƙungiyar na jiha.

Da yake jawabi bayan Barista Fatima Enegi ta jagoranci rantsar da sabbin shugabannin, shugaban NUMW na Jihar Neja, Kwamared Musa Adamu Nasko, ya buƙace su da su kasance jagorori na gari tare da haɗa kan mambobin ƙungiyar da kuma tabbatar da gudanar da ayyukansu bisa tanadin doka.

Ya ce duk wanda aka samu da laifin gudanar da aiki saɓanin dokokin ƙungiyar, ba zai samu kariya daga NUMW ba, domin ƙungiyar tana ƙarƙashin Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), kuma an yi mata rajista ne bisa dokokin ƙasa. Saboda haka, ya ce ƙungiyar ba za ta amince da duk wani aiki da ya saɓa wa doka ba, musamman amfani da yara masu ƙasa da shekara 18 wajen aikin haƙar ma'adinai.

Shugaban ya kuma bayyana cewa, duk da ƙalubalen da suka jinkirta gudanar da zaɓen shugabannin, ya kamata sabbin shugabannin su ɗauki hakan a matsayin darasi, su rungumi kowa domin ci gaban ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa ya zama wajibi su ci gaba da aikin tattara bayanan mambobin ƙungiyar (Data Capture), wanda ya ce ba Jihar Neja kaɗai ake aiwatarwa ba, illa wani shiri ne na uwar ƙungiyar da ake gudanarwa a dukkan jihohin Najeriya.

A cewarsa, idan shugabannin suna son sake neman wa'adi na biyu bayan karewar shekaru huɗu na wa'adinsu, dole ne su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata domin samun amincewar mambobi da kuma bin ƙa'idojin kundin tsarin mulkin ƙungiyar.

Da yake jawabi ga manema labarai, sabon shugaban reshen Paikoro, Alhaji Yakubu Musa, ya yabawa shugabancin NUMW na Jihar Neja bisa jajircewarsu wajen tabbatar da an gudanar da zaɓen duk da ƙalubalen da aka fuskanta.

Ya ce, "A yau duniya ta shaida cewa mu ne halastattun shugabannin reshen Paikoro. Za mu gudanar da ayyukanmu cikin gaskiya da riƙon amana tare da bin dokokin ƙungiya da na ƙasa."

Ya ƙara da cewa an bai wa dukkan shugabannin kundin tsarin mulkin ƙungiyar da kuma tsare-tsaren gudanar da aiki, don haka babu wanda zai yi hujjar cewa bai san dokokin ƙungiyar ba.

Alhaji Yakubu ya yi kira ga dukkan mambobin ƙungiyar da su haɗa kai domin ciyar da harkokin haƙar ma'adinai gaba a Paikoro.

"Da yardar Allah, idan muka haɗa kai, cikin shekaru huɗu Paikoro za ta kasance a sahun gaba wajen bunƙasa harkokin haƙar ma'adinai a Jihar Neja," in ji shi.

Ita ma zababbiyar shugabar mata ta reshen Paikoro, Hajiya Hulera Sani Ibrahim, ta ce mata na taka muhimmiyar rawa a harkar haƙar ma'adinai, don haka za ta yi amfani da damar da aka ba ta wajen ƙarfafa gwiwar mata domin su ci gaba da shiga harkar.

Ta ce shigar mata cikin aikin haƙar ma'adinai ya taimaka wa iyalai da dama wajen samun abin dogaro da kai, musamman iyalan da mata ke taimakawa wajen ciyar da gida, biyan kuɗin karatun yara da sauran buƙatun rayuwa.

Shi ma mataimakin shugaban reshen, Alhaji Haruna Tanko, ya yi kira ga waɗanda suka nemi mukamai amma ba su yi nasara ba da su rungumi sakamakon zaɓen cikin haƙuri da fahimta, yana mai cewa rashin nasara ma wata hanya ce ta samun ƙwarewa.

Ya ce, "Mu matasa burinmu shi ne mu ga matasa sun dogara da kansu. A ƙarƙashin jagorancin Alhaji Yakubu Musa, za mu yi aiki tuƙuru wajen haɗa kan dukkan ma'aikatan ma'adinai a Ƙaramar Hukumar Paikoro."

Ya kuma bayyana cewa matsalolin da ake samu a baya tsakanin jami'an tsaro da masu aikin haƙar ma'adinai sun samo asali ne daga rashin ingantaccen shugabanci da kuma ƙarancin sanin dokokin aiki.

A cewarsa, yanzu da aka samu ingantaccen shugabanci, za su yi aiki tare da shugabancin jiha, jami'an tsaro da sarakunan gargajiya domin tabbatar da tsafta da bin doka a harkar haƙar ma'adinai a Ƙaramar Hukumar Paikoro.

Post a Comment

Previous Post Next Post