TGCG Ta Sha Alwashin Tabbatar da Nasarar APC a Zaɓe Mai Zuwa

Daga Awwal Umar Kontagora

Ƙungiyar The Game Changer Group (TGCG) ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa domin ganin jam'iyyar APC ta samu nasara a zaɓe mai zuwa.

Kodinetan ƙungiyar na Jihar Neja, Hon. Umar Abdullahi Gwandu Wushishi, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar na jihar.

Hon. Gwandu ya ce, duba da manufofi da ayyukan da gwamnatin APC ke aiwatarwa daga matakin tarayya zuwa jihohi da ƙananan hukumomi, akwai buƙatar ƙara wayar da kan al'umma kan nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da kuma gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin Gwamna Umaru Mohammed Bago wajen aiwatar da manufar "Sabuwar Jihar Neja (New Niger)."

Ya bayyana cewa saboda haka ne ƙungiyar ta zaƙulo mutane masu hangen nesa da kishin ƙasa domin ba su damar taka rawa wajen cimma wannan buri.

A cewarsa, tafiyar TGCG ba ta 'yan siyasa kaɗai ba ce, illa tafiya ce ta kowa da kowa. Ya ce an zaɓi mutane daga fannoni daban-daban da suka haɗa da tsaro, aikin gwamnati da masu fafutukar ci gaban al'umma domin su taimaka wajen tabbatar da ci gaban ƙasa ta hanyar ci gaba da tallata ayyukan alherin gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hon. Gwandu ya ƙara da cewa, bisa wannan manufa ne ƙungiyar ta zaɓi Gwamna Umaru Mohammed Bago da Comrade Idris Abdulkareem Lafene (Hasken Wushishi) a matsayin iyayen ƙungiyar, sakamakon irin gudummawar da suke bayarwa wajen kawo sauyi a salon shugabanci.

Ya ce gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin Gwamna Umaru Mohammed Bago ta aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa da za su ci gaba da kasancewa abin alfahari a tarihin jihar. A cewarsa, waɗannan ayyuka sun yi daidai da manufar "New Niger" da gwamnan ke ƙoƙarin tabbatarwa.

A nata jawabin, shugabar mata ta ƙungiyar a jihar, Hajiya Rukayyah I. Bature, ta yabawa gwamnatin Umaru Mohammed Bago bisa samar da damammaki ga mata. Sai dai ta nuna damuwa cewa duk da irin rawar da mata suka taka a zaɓukan baya, ba su samu wakilci da damar da suka dace ba.

Ta bayyana fatan cewa gwamnati za ta yi amfani da shawarwarin da ƙungiyar TGCG za ta bayar domin inganta wakilcin mata a muƙaman gwamnati.

Hajiya Rukayyah ta kuma yi kira ga mata da su fito su yi rajista tare da karɓar katin zaɓe, domin su ci gaba da mara wa jam'iyyar APC baya a zaɓe mai zuwa.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, ɗaya daga cikin iyayen ƙungiyar, Comrade Idris Abdulkareem Lafene (Hasken Wushishi), ya ce siyasa gwagwarmaya ce, kuma bai dace a riƙa watsi da ayyukan alheri saboda wasu ƙalubale da ƙasa ke fuskanta ba.

Ya ce duk da matsalolin tattalin arziki, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin Gwamna Umaru Mohammed Bago sun samu nasarori da dama da ya kamata a yaba musu.

Ya ƙara da cewa matasan da suka kafa The Game Changer Group sun nuna hangen nesa da kyakkyawan tunani, abin da ya rage shi ne a ba su cikakken goyon baya da ƙarfafa guiwa. Ya jaddada cewa tafiyar TGCG ba ta Jihar Neja kaɗai ba ce, illa tafiya ce ta ƙasa baki ɗaya.

Game da saɓanin da ake samu tsakanin wasu shugabannin siyasa a jihar, Comrade Lafene ya ce samun bambancin ra'ayi abu ne da ke faruwa a siyasa, kuma hakan ba alamar gazawa ba ce, sai dai wata dama ta gyara kura-kurai da ƙarfafa haɗin kai.

Ya kuma tabbatar da cewa a matsayinsu na iyayen ƙungiyar, za su tabbatar da cewa duk wanda ya ba da gudummawa wajen samun nasarar jam'iyyar APC ba za a manta da shi ba idan aka kafa gwamnati bayan zaɓe.

A ƙarshe, Comrade Idris ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ci gaba da haƙuri tare da bai wa gwamnatin APC goyon baya, yana mai cewa ajandar gwamnatin ita ce ciyar da ƙasa gaba da samar wa al'umma ingantacciyar rayuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post