SPAK II Ya Mayar da Hankali Wajen Inganta Fannin Kiwon Lafiya a Jihar Neja

Daga Awwal Umar Kontagora

Tun bayan da gwamnatin tarayya ta tsawaita wa'adin aiwatar da shirin SPAK II, ƙungiyar FOMWAN tare da International Budget Partnership (IBP) sun ƙara mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin al'umma da jami'an kiwon lafiya domin inganta ayyukan cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko a Jihar Neja.

Kodinetan shirin SPAK II a Jihar Neja, Hajiya Aishatu Ibrahim Lemu, ta bayyana cewa haɗin gwiwar da suke yi da IBP ya fi karkata ne wajen inganta ayyukan Cibiyoyin Kula da Lafiya na Matakin Farko (Primary Healthcare Centres), domin tabbatar da cewa mata, masu juna biyu, masu shayarwa da kuma masu buƙata ta musamman suna samun ingantacciyar kulawar lafiya cikin sauƙi.

Ta ce babban abin da shirin ya fi mayar da hankali a kai shi ne wayar da kan al'umma da kuma ƙarfafa kyakkyawar alaƙa tsakanin jama'a da jami'an kiwon lafiya, domin tabbatar da cewa masu buƙatar kulawa suna samun ingantattun ayyukan lafiya ba tare da tsoro ko wata tangarda ba.

A cewarta, a wannan karo an shirya taron yini guda da ya haɗa mambobin Ward Development Committee (WDC), jami'an kiwon lafiya da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa fahimtar juna da kuma inganta haɗin gwiwa wajen cimma manufofin gwamnati a fannin kiwon lafiya.

Da yake jawabi, Daraktan Gudanarwa na Hukumar NiCARE ta Jihar Neja, Attahiru Shehu Malagi, ya ce babban burinsu shi ne tabbatar da cewa kuɗaɗen da gwamnati ke warewa domin gudanar da ayyukan cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko ana amfani da su yadda ya kamata kuma bisa ga buƙatun al'umma.

Ya bayyana cewa idan aka gano wata matsala, ana fara ba da gargaɗi, idan kuma ba a gyara ba sai a nemi bayani a rubuce. Idan aka ci gaba da samun sakaci ko rashin bin ƙa'ida, hukumar ba ta yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukar matakin ladabtarwa kan duk wani jami'in da aka samu da laifi.

A cewarsa, manufar wannan shiri ita ce inganta ayyukan cibiyoyin kula da lafiya da ke kusa da al'umma, musamman domin sauƙaƙa wa mata masu juna biyu, masu shayarwa, marasa galihu da masu buƙata ta musamman samun ingantaccen sabis na kiwon lafiya.

Ya ƙara da cewa shirin yana da matuƙar muhimmanci, saboda yana taimakawa wajen gina kyakkyawar fahimta tsakanin wakilan al'umma da jami'an kiwon lafiya, abin da ke taimakawa wajen haɓaka ingancin ayyukan lafiya.

A nata jawabin, Mataimakiyar Darakta mai kula da wayar da kai ta Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Neja, Aishatu J. Yahaya, ta ce wannan shiri ba sabon abu ba ne, sai dai wani ci gaba ne na ƙoƙarin ƙarfafa tsarin sa ido da tantance yadda ayyukan cibiyoyin kula da lafiya ke gudana.

Ta bayyana cewa shirin yana bai wa wakilan al'umma damar bibiyar yadda ake kula da marasa lafiya, yadda jami'an lafiya ke gudanar da ayyukansu da kuma yadda ake amfani da kuɗaɗen da gwamnati ke warewa domin bunƙasa ayyukan kiwon lafiya.

A ƙarshe, ta jaddada cewa samun fahimtar juna tsakanin jami'an kiwon lafiya da wakilan al'umma masu sanya ido na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaba da inganta fannin kiwon lafiya a Jihar Neja.

Post a Comment

Previous Post Next Post