Daga Wakilinmu
Bangaren Dandalin Resource na Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta bayyana shahadar tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Sayyid Ali Khamene'i, a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi ta duniya, tana mai cewa rayuwarsa ta kasance cike da imani, hidima, adalci da kuma jagoranci mai cike da tsayin daka.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, shugaban Resource Forum, Farfesa Abdullahi Danladi, ya yi ta'aziyyar rasuwar marigayin gabanin bizne shi da aka tsara gudanarwa ranar 9 ga Yulin 2026, bayan kammala jerin tarukan tunawa da shi da ake gudanarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma Jamhuriyar Iraki.
Farfesa Danladi ya ce shahadar “manyan malamai da shugabanni masu riƙo da manufa” ba wai tana haifar da giɓin shugabanci kaɗai ba ne, har ma tana barin babban giɓin ɗabi’a da ilimi a cikin al’umma.
A cewarsa, Sayyid Ali Khamene'i ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen yi wa addinin Musulunci hidima, neman tabbatar da adalci da kuma kare mutunci da 'yancin kan al'ummar Iran.
Ya ce, “Fiye da shekaru talatin, ya jagoranci Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin manyan ƙalubalen siyasa, tattalin arziki da na soja. Duk da takunkumai, barazana da matsin lamba daga ƙasashen waje, ya ci gaba da tsayawa kan akidunsa tare da kare abin da ya yi imani da cewa haƙƙin al’ummarsa ne da kuma waɗanda ake zalunta.”
Danladi ya ƙara da cewa jajircewar Khamene’i, ƙudirinsa da kuma tsayin dakarsa kan gaskiya sun sa ya samu girmamawa da karɓuwa har fiye da iyakokin ƙasar Iran.
Ya kuma ce tarihi yana tuna shugabanni “ba don muƙaman da suka riƙe ba, sai dai saboda manufar da suka tsaya a kansu,” yana mai cewa mutane al’umma da dama za su ci gaba da tuna Khamene'i “a matsayin alamar juriya, ƙin mamaya da kuma amincewa da cewa Musulunci na da ikon jagorantar al’umma wajen fuskantar ƙalubalen duniyar zamani.”
Da yake kawo aya ta 185 a Suratu Ali Imran, Danladi ya tunatar da Musulmi cewa, “Kowace rai mai ɗanɗanar mutuwa ce,” yana mai cewa mutuwa makoma ce da babu makawa ga kowane ɗan Adam.
Ya ce, “Abin da ke bambanta mutum ba mutuwarsa ba ce, illa ƙimomin da ya rayu a kansu da kuma kyakkyawan abin da ya bari a bayansa. Kamar yadda muka ƙaunaci Sayyid Ali Khamene'i, Allah Ya fi mu ƙaunarsa. Don haka muna miƙa wuya ga hukuncin Allah cikin haƙuri da imani.”
Danladi ya miƙa ta'aziyya ga shugabanci da al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, iyalan marigayin, jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, al’ummar Musulmi ta duniya da kuma duk waɗanda suka samu kwarin gwiwa daga rayuwa da jagorancin marigayin.
Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya karɓi dukkan hidimomin da Khamene'i ya yi wa addini, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya ba shi mafificin matsayi a Aljanna, tare da bai wa duk masu jimamin rasuwarsa haƙuri da juriya.
Da yake kammala jawabinsa, Danladi ya kawo aya ta 156 a Suratul Baƙara, wadda ke cewa: “Lalle mu na Allah ne, kuma gare Shi za mu koma,” yana mai addu'ar Allah Ya sanya abin alherin da marigayin ya bari ya ci gaba da kasancewa tushen shiriya da abin koyi ga al’ummomi masu zuwa.
Post a Comment