An Gudanar da Taron Tunawa da Shahidan Ƙudus na 2014 Karo na 12 a Zariya

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya gabatar da jawabi a wajen taron tunawa da Shahidan waƙi'ar Ƙudus ta ranar 25 ga Yulin 2014, wanda aka gudanar a yau Asabar, 25 ga Yuli, 2026, a muhallin Darur Rahma da ke Dambo, Zariya.

A farkon jawabinsa, Jagoran ya nuna alhini kan waƙi'ar Ashura da kuma wafatin Imam Hassan Mujtaba (A.S), tare da tunatar da al'umma game da kusantowar Arba'in da kuma tunawa da Shahid Sayyid Ali Khamene'i (RH).

Ya bayyana cewa taron na bana ya cika shekaru 12 cif-cif da aukuwar harin da aka kai wa masu gudanar da muzaharar ranar Ƙudus a ranar 25 ga Yulin 2014, wanda ya yi daidai da 28 ga Ramadan, 1435H, yana mai cewa manufar taron ita ce ci gaba da raya tunawa da shahidan wannan waƙi'a. 

Shaikh Zakzaky ya kuma waiwayi tarihin fara gudanar da muzaharar ranar Ƙudus a Najeriya, yana mai cewa an fara ne a Zariya a Juma'ar ƙarshe ta watan Ramadan, kafin daga bisani ta bazu zuwa sassa daban-daban na ƙasar sakamakon ƙaruwa da yawan masu halarta.

Ya ce muzaharar Ƙudus ta duniya wata hanya ce ta nuna goyon baya ga al'ummar Falasɗinu da kuma nuna ƙin amincewa da zaluncin da suke fuskanta tsawon shekaru.

Da yake tsokaci kan harin da aka kai wa muzaharar Ƙudus a shekarar 2014, Jagoran ya ce wannan shi ne karo na farko da aka kai wa irin wannan muzahara hari a duniya. Ya ƙara da cewa, duk da abin da ya faru a wancan lokaci da kuma abubuwan da suka biyo baya, hakan ba zai hana mabiyansa ci gaba da gudanar da muzaharar ba.

Shaikh Zakzaky ya jaddada cewa ba za a tsorata su da barazanar mutuwa ba, yana mai cewa ci gaba da bin tafarkin da shahidan suka sadaukar da rayuwarsu a kai shi ne abin da suka ɗauka a matsayin alƙawari.

Har ila yau, ya yi kira ga waɗanda suka aikata kisan kiyashin da su tuba, yana mai gargadin cewa idan ba su tuba ba, za su fuskanci hasara a duniya da lahira.

A ƙarshe, Jagoran ya bayyana cewa taron tunawa da shahidan alama ce ta ƙauna da girmamawa ga waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu a wannan tafarki, yana mai cewa ci gaba da tuna su wani nau'i ne na girmama sadaukarwarsu.

Bayan kammala jawabin, Shaikh Zakzaky ya gaisa da malamai, fastoci, sauran baƙi da aka gayyata da kuma iyalan shahidan. Daga nan ya jagoranci ziyarar ƙaburburan shahidan da ke Darur Rahma kafin daga bisani aka kammala taron da addu'a.

Tun da farko, an buɗe taron da addu'a da karatun Alƙur'ani Mai Girma, sannan aka gabatar da faretin girmama shahidai, wasannin kwaikwayo da nune-nunen da suka shafi waƙi'ar Ƙudus ta 2014.

Post a Comment

Previous Post Next Post