Daga Awwal Umar Kontagora
Cibiyar Markazil Dirāsatil Islāmiyya, wadda aka fi sani da Islamic Education Centre, da ke unguwar Airport Quarters a Minna, ta gudanar da bikin dalibai 25 da ke shirin gudanar da walimar saukar Alƙur'ani mai girma a farkon watan Agustan bana.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin shirya walimar, Alhaji Mohammed Ndanusa Gaba, ya bayyana cewa manufar bikin ita ce neman albarka ga daliban da ke shirin saukar Alƙur'ani tare da yi musu addu'o'i daga manyan malamai. Ya ce wannan al'ada ce da cibiyar ke gudanarwa duk lokacin da ake shirin walima, kuma ba shi ne karon farko ba.
Ya ƙara da cewa, tun bayan kafuwar cibiyar ba ta taɓa karɓar kuɗin wata ko na mako daga ɗalibai ba. A cewarsa, cibiyar ta horar da daruruwan yara, matasa da mata a fannin ilimin addinin Musulunci. Saboda haka, ya yi kira ga iyaye da sauran masu hannu da shuni da su tallafa wa cibiyar domin ta ci gaba da koyar da ilimi da kuma gina kyawawan ɗabi'u a tsakanin al'umma.
Shi ma wanda ya assasa cibiyar kuma shugaban ta, Malam Muhammad Ibrahim Gaba, wanda aka fi sani da Malam Babba, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa nasarorin da cibiyar ta samu tsawon shekaru. Ya ce ba wannan ne karon farko da cibiyar ke gudanar da walimar saukar Alƙur'ani ba, domin ɗalibai da dama daga sassa daban-daban na Minna sun yi karatu a cikinta, kuma wasu daga cikinsu sun zama malamai masu koyarwa.
Malam Babba ya yi kira ga iyaye da su ba da muhimmanci ga tarbiyyar 'ya'yansu, yana mai cewa tarbiyyarsu amana ce da Allah Ya ɗora musu. Ya buƙaci su tabbatar sun koyar da 'ya'yansu ilimin addini, tare da ba su ilimin zamani da kuma sana'o'in hannu domin su zama masu amfani ga kansu da al'umma.
Haka kuma, ya yabawa malaman cibiyar bisa sadaukarwar da suke yi wajen koyarwa ba tare da biyan albashi ba. Ya ce wannan babban aikin alheri ne da mutum zai ci gaba da cin moriyarsa ko bayan rasuwarsa.
A nasa jawabin, Malam Muhammad Abubakar, wanda ya jagoranci bikin daliban, ya ce irin wannan taro na ƙara kusantar da iyaye da malamai tare da ƙarfafa gwiwar dalibai wajen neman ilimin addini.
Ya tunatar da jama'a wasu daga cikin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), inda ya ce ya kamata iyaye su koyar da 'ya'yansu Alƙur'ani, su koyar da su sana'o'in hannu, sannan idan sun kai lokacin aure su aurar da su.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda wasu iyaye ke ba da fifiko ga ilimin zamani fiye da na addini. A cewarsa, ya dace iyaye su riƙa ba ilimin addini muhimmanci kamar yadda suke yi wa ilimin zamani, domin ilimin addini shi ne ginshiƙin rayuwar duniya da lahira.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa cibiyar ba ta sanya wani takamaiman kuɗin karatu ga ɗalibai ba, akwai buƙatar iyaye da sauran al'umma su ba ta gudummawa domin tabbatar da dorewar ayyukanta.
Shi ma Barrista M. B. Shehu, wani lauya, ya yabawa jagororin cibiyar, musamman Malam Babba, saboda jajircewarsa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci da kuma tarbiyyar mata da matasa.
Ya kuma jinjinawa malaman cibiyar bisa sadaukarwar da suke yi wajen koyarwa ba dare ba rana, duk da cewa ba sa karɓar albashi, domin tabbatar da cewa matasa sun samu ingantacciyar tarbiyyar addini.
An kafa cibiyar ne shekaru da dama da suka gabata, kuma ta samar da ɗalibai masu yawa, inda wasu daga cikinsu suka zama malamai masu koyarwa a cikinta.
A ƙarshe, hukumomin cibiyar sun sanar da cewa za a gudanar da walimar saukar Alƙur'ani ta dalibai 25 ranar 1 ga Agusta, 2026, a harabar cibiyar da ke unguwar Airport Quarters a garin Minna.
Post a Comment