N-HYPPADEC Ta Raba Kayan Tallafi Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Jihar Kwara

Daga Awwal Umar Kontagora

Hukumar Raya Yankunan da ke Samar da Wutar Lantarki ta Ƙasa (N-HYPPADEC) ta ƙaddamar da rabon kayan tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa, tare da raba kayan aikin gona ga manoma a ƙananan hukumomin Baruten, Edu, Kaima, Moro da Patigi na Jihar Kwara.

Shirin na da nufin tallafa wa manoman da suka yi asara mai yawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi ayyukan noma a shekarar 2025. Haka kuma, ana sa ran kayan aikin gonar da aka raba za su taimaka wajen bunƙasa ayyukan noma da inganta rayuwar al'umma a faɗin ƙananan hukumomin N-HYPPADEC guda biyar da ke Jihar Kwara.

Babban Daraktan N-HYPPADEC, Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa, FCNA, FNIM, FNIIS (Katukan Yauri), ne ya ƙaddamar da rabon kayayyakin tare da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda Kwamishinar Ma'aikatar Kiwon Dabbobi da Bunƙasa Ayyukan Gona, Misis Adebayo Olorunnimbe, ta wakilta.

Taron ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Tsonga, HRH Dr. Haliru Yahaya Ndanusa, CON, da wakilin Sarkin Patigi, tare da shugabannin ƙananan hukumomin Kaima, Edu, Moro da Baruten.

Waɗanda suka amfana da tallafin sun yaba da wannan shiri na N-HYPPADEC, tare da tabbatar da cewa za su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata domin bunƙasa ayyukansu na noma da inganta rayuwarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post