NRS da NUMW Za Su Haɗa Hannu Domin Bunƙasa Kuɗaɗen Shigar Gwamnati

Daga Awwal Umar Kontagora

Hukumar Nigeria Revenue Service (NRS) da Nigeria Union of Mines Workers (NUMW) sun cimma matsayar yin aiki tare domin bunƙasa kuɗaɗen shigar gwamnati.

An cimma wannan matsaya ne bayan wani taron fahimtar juna da aka gudanar tsakanin hukumar da ƙungiyar a sakatariyar hukumar da ke Minna, babban birnin Jihar Neja, a safiyar Litinin.

Da yake jawabi ga shugabannin NUMW, Konturolan Hukumar NRS, Malam Aliyu Ango, ya buƙaci shugabannin ƙungiyar da su wayar da kan mambobinsu game da sabon tsarin biyan haraji da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar, domin tabbatar da tsabtar bayanan kuɗaɗen shigarsu tare da kauce wa duk wani abin da ka iya zama barazana ga kuɗaɗen shigar gwamnati.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da nazarin matsalolin da ke hana kuɗaɗen shiga isa inda ya kamata, tare da samar da hanyoyin magance su bisa sabon tsarin da gwamnati ta amince da shi.

Malam Aliyu Ango ya kuma yaba wa shugabannin ƙungiyar bisa haɗin kan da suke bai wa hukumar, yana mai bayyana cewa yin aiki tare zai taimaka wajen bunƙasa harkokin haƙar ma'adinai da ƙara wa gwamnati kuɗaɗen shiga domin ci gaban ƙasa.

A nasa jawabin, Shugaban NUMW na Jihar Neja kuma Mataimakin Ma'ajin Ƙasa na ƙungiyar, Kwamared Musa Adamu Nasko, ya gode wa hukumar bisa gayyatar da ta yi musu, yana mai tabbatar da cewa ƙungiyar a shirye take ta mara wa duk wani shiri na ci gaban ƙasa baya, musamman ta fuskar zaman lafiya, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arziƙin al'umma.

Sai dai ya bayyana cewa akwai wasu ƙalubale da ke buƙatar kulawar hukumar tare da haɗin gwiwa da Ma'aikatar Ma'adinai, musamman domin kauce wa tilasta wa masu haƙar ma'adinai biyan kuɗaɗen shiga sau biyu.

Ya ce: "Muna amfani da tsarin Cooperative da gwamnati ta amince da shi, wanda Ma'aikatar Ma'adinai ke gudanarwa, kuma a ƙarƙashinsa muke biyan kuɗaɗen shigarmu ga gwamnati. Yanzu kuma an bullo da sabon tsarin rajistar Corporate Affairs Commission (CAC). Idan aka tilasta wa mambobinmu yin rijistar CAC tare da ci gaba da bin tsohon tsarin, hakan zai zama tamkar an tilasta musu biyan kuɗaɗen gwamnati sau biyu."

Nasko ya buƙaci hukumar da ta saurari ƙorafe-ƙorafen ƙungiyar domin a samu kyakkyawar fahimtar juna da haɗin gwiwa, ta yadda gwamnati za ta ci gaba da samun kuɗaɗen shiga yadda ya kamata domin gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Ya ƙara da cewa ma'aikatan ma'adinai na daga cikin masu bin doka da oda, yana mai jaddada cewa ƙungiyar za ta ci gaba da wayar da kan mambobinta kan bin dokokin ƙasa da kuma ba gwamnati cikakken goyon baya.

A ƙarshen taron, Konturolan Hukumar NRS ya miƙa wa shugabannin ƙungiyar kundayen bayanai kan sabon tsarin biyan kuɗaɗen shiga na shekarar 2025, domin su ƙara fahimtar yadda tsarin zai gudana.

Post a Comment

Previous Post Next Post