Huffazul Qur'an Ta Gudanar Da Addu'o'in Zaman Lafiya Ga Ƙasa Karo Na Tara A Minna

Daga Awwal Umar Kontagora

Ƙungiyar Huffazul Qur'an and Scholars Association of Nigeria reshen Jihar Neja ta gudanar da addu'o'in neman zaman lafiya ga Jihar Neja da Najeriya karo na tara a birnin Minna, domin roƙon Allah Ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro tare da bai wa ƙasa shugabanci nagari.

Da yake jawabi, Shugaban ƙungiyar a Jihar Neja, Sheikh Hussaini Abubakar Shakwata, ya bayyana cewa an shafe shekaru tara ana gudanar da wannan shiri, wanda manufarsa ita ce komawa ga Allah da addu'a domin neman mafita ga ƙalubalen da jihar da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce ɗaliban makarantun tsangaya daga sassa daban-daban na jihar ne suka halarci taron bayan kammala saukar Alƙur'ani Mai Tsarki, inda manyan malamai suka jagoranci addu'o'in.

Sheikh Shakwata ya kuma bayyana cewa ƙungiyar na shirin samar da kayan sawa (uniform) ga makarantun tsangaya a faɗin jihar domin tantance su, tare da ƙarfafa haɗin kai da inganta tsarin gudanar da makarantun.

Ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara tallafa wa irin waɗannan shirye-shiryen addini, yana mai cewa karatun Alƙur'ani da addu'a na taka muhimmiyar rawa wajen neman mafita ga matsalolin al'umma.

Shi ma Kodinetan Tsangaya na yankin Neja ta Arewa, Alhaji Ibrahim Wushishi, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa komawa ga Allah ta hanyar karatun Alƙur'ani da addu'a ita ce hanya mafi dacewa wajen neman mafita ga ƙalubalen rayuwa.

Ya buƙaci sauran ƙungiyoyi su yi koyi da wannan tsari, tare da kira ga gwamnati da ta mara wa irin waɗannan ayyukan baya.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar 'Yan Kasuwan Minna, Kwamared Zubairu Mohammed, ya bayyana cewa ƙungiyarsa na goyon bayan wannan shiri saboda muhimmancin zaman lafiya ga harkokin kasuwanci.

Ya ce matsalar tsaro ta fi shafar 'yan kasuwa, don haka duk wata hanya ta halal da za ta taimaka wajen neman zaman lafiya ta cancanci a tallafa mata. Haka kuma ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa ƙungiyar domin ci gaba da gudanar da irin waɗannan ayyukan alheri.

Taron ya samu halartar wakilan ƙungiyoyin Musulunci daban-daban, ciki har da Tijjaniyya, Izala (Jos da Kaduna), da kuma mabiya Sheikh Ibraheem Zakzaky.

Post a Comment

Previous Post Next Post