KAWO ƘARSHEN HARKA MAFARKI NE DA BA ZAI YIWU BA — Jagora Shaikh Zakzaky (A) A Taron Tunawa Da Shekaru 30 Da Waƙi'ar Abacha

A ranar Asabar, 12 ga Satumba 2026, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin tunawa da cika shekaru 30 da Waki’ar Abacha, a gidansa da ke Abuja. A yayin bitar waki’ar, Jagora (H) ya bayyana waƙi’ar a matsayin wani tsararren shiri da aka ƙulla da nufin kawo ƙarshen Harka Islamiyya a wancan lokacin. Ya ce, sun tsara shirin ne da farawa da kamu, sannan a murƙushe masu gudanar da muzaharori. Bayan nan idan aka yi tsit, sai su aiwatar da kisa, da nufin kawo ƙarshen Harka gabaɗaya. 

Shaikh Zakzaky (H) ya bayyana cewa, tsayuwar ƴan uwa, kiraye-kirayen jama'a ciki da wajen Nijeriya, da ci gaba da gudanar da Muzaharori, tare da tunkarar zaluncin azzalumai duk da muzgunawa da cutarwa, musamman ƴan uwa da ake kira Ƴan Caji-caji, su ne suka hana aiwatar da wannan mummunan shiri. Yace, tunanin maƙiya na kawo ƙarshen Harka Islamiyya “mafarki ne da ba zai taɓa yiyuwa ba.” 

Ya ƙara da cewa, Harka ita ce mafita ga al’umma, kuma addini zai tabbata, in sha Allah.  Jagora (H) ya bayar da tarihin Waki'ar, yadda ta faro, da abubuwa daban-daban da ta kunsa, zuwa karshenta da kuma jaza'in da wadanda suka aukar da ita suka girba. Ya kuma jaddada cewa, barazanar mahukunta ba za ta sa mu bar gwagwarmayar tabbatar addini ba. 

A bana ne ake cika shekaru 30 cur da Waki'ar Abacha, wadda ta fara aukuwa a rana irin ta yau, 12 ga Satumba 1996. An gudanar da tarukan Zikiran Waki'ar a ranakun Alhamis da Juma'a a garin Zaria, Kaduna da Saminaka, kafin daga bisani a rufe a yau Asabar a Abuja. 

Post a Comment

Previous Post Next Post