Wani rahoto da jaridar Globes ta wallafa ya nuni da cewa kamfanoni da dama a Isra’ila na fuskantar matsananciyar matsalar kuɗi, inda wasu ke dab da durƙushewa bayan shekaru biyu suna karɓar sabbin lamuni domin biyan tsofaffin basussukansu.
Rahoton ya ce kamfanonin gine-gine sun fi fuskantar ƙalubale sakamakon raguwar masu zuba jari da tsadar gudanar da ayyuka.
A cewar Babban Bankin Isra’ila, yaƙe-yaƙen da ƙasar ke yi tun daga 2023 sun jawo asarar sama da shekel biliyan 352, yayin da yaƙin Gaza kaɗai ya lakume kusan shekel biliyan 150.
Masana sun ce yawan kashe kuɗaɗen soji da ci gaba da rikice-rikicen yankin na ƙara jefa tattalin arziƙin Isra’ila cikin matsin lamba, tare da barazana ga dorewar wasu manyan kamfanoni.

Post a Comment