A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce duk zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin na buƙatar samun amincewa da haɗin kai da hukumomin Iran saboda muhimmancin hanyar ruwa ga kasuwancin duniya.
Iran ta sake jaddada cewa ba za ta buɗe mashigin Hormuz gaba ɗaya ba har sai an ɗage takunkumin da ta kira na haramtacciyar katanga ta ruwa da kuma tabbatar da ƙarshen yaƙin da ake yi a yankin.
Mashigin Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai da iskar gas a duniya, inda kusan kashi ɗaya cikin biyar na makamashin duniya ke ratsawa ta cikinsa.

Post a Comment