An sake sanya Rawani ga almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) 10 da ke karatu a ƙasar Iraqi bayan kai wani mataki da sukayi na karatu.
Taron sanya Rawanin ya gudana cikin farin ciki da murna da kaiwa wannan mataki, an musu nasiha kan girmama nauyin da ya hau kansu na ɗora wannan babban matsayi, an je kunnensu da su zama masu hidima ga addinin Allah da kuma bayinsa.
Mutum 10 da aka sanyawa Rawanin sun haɗa da ɗaliban da ke karatu a Najaf irin su; Sheikh Ali Zakariyya, Sheikh Ibrahim Shu’aibu, Sheikh Surajo Muhammad, Sheikh Yakubu Usman, Sheikh Yahaya Muhammad, da kuma Sheikh Zayyanu Idriss.
Sai ɗalibai huɗu da ke karatu a Karbala wanda ya haɗa Sheikh Mustapha Siddi, Sheikh Adam Hajj Ibrahim, Sheikh Abdulhayy Ridwan da Sheikh Muhammad Isa Bukar.
Dandalin yaɗa labarai na Harkar Musulunci – Iraq Team.

Post a Comment