Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya janye shirin kai sabon hari kan birnin Beirut na ƙasar Lebanon bayan gargaɗin da Iran ta yi cewa ba za ta lamunci ci gaba da kai hare-hare kan Lebanon ba, a cewar Shugaban Amurka, Donald Trump.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, Trump ya ce ya yi wata tattaunawa mai amfani da Netanyahu, wanda tun da fari ya sanar da cewa ya umarci sojojin Isra’ila su kai hare-hare a yankin Dahiyeh da ke kudancin Beirut.
Trump ya bayyana cewa an dakatar da shirin tura sojoji zuwa Beirut, yana mai cewa duk wasu dakaru da aka tura sun koma baya bayan tattaunawar da aka yi.
Shugaban na Amurka ya kuma yi iƙirarin cewa ya samu fahimta da ƙungiyar Hi/zb/ull/ah ta Lebanon ta hanyar wasu wakilai, inda ya ce ɓangarorin sun amince da dakatar da musayar hare-hare tsakaninsu.
Wannan ci gaba ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan manyan hafsoshin sojin Iran sun yi gargaɗi ga Isra’ila kan duk wani yunƙurin kai hari a kudancin Beirut. Hedikwatar Sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta bayyana cewa idan Isra’ila ta aiwatar da barazanar kai hari, mazauna yankunan arewacin ƙasar da kuma matsugunan sojoji a yankunan da Isra’ila ke iko da su su shirya ficewa domin kauce wa haɗari.
Iran ta ci gaba da jaddada cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ce Pakistan ta taimaka wajen samarwa tsakanin Tehran da Washington a ranar 8 ga Afrilu ta shafi dukkan wuraren rikici, ciki har da Lebanon.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya sake nanata cewa duk wani hari a Lebanon zai kasance karya yarjejeniyar tsagaita wutar gaba ɗaya, yana mai gargadin cewa duk wanda ya karya yarjejeniyar zai ɗauki alhakin sakamakon da zai biyo baya.

Post a Comment