Iran ta janye daga tattaunawar da su ke da Amurka bayan harin Isra'ila a Lebanon


Iran ta dakatar da tattunawar da take da Amruka kan rikicin da ke tsakaninsu biyo bayan jerin hare-haren da Isra’ila ta kai cikin Lebanon da yammacin jiya litinin.

A cewar kafofin yada labaran Iran gwamnati ta yanke shawarar ne don nuna hushi kan yadda dakarun Isra'ila ke cigaba da yin  luguden wuta a kudancin Lebanon abin da ke barazana ga ƙwarya-ƙwaryar zaman Lafiyar da aka samu a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Tasnim ya ce nan gaba kadan Téhéran za  ta bukaci wakilanta a tattunawar da su dakatar da musayar sakonni tsakaninsu da takwarorinsu na Amurka ta hanyar masu shiga tsakani.

Tun da fari dai Iran ta ce ba zai yiyu a cimma duk wata yarjejeniyar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ba tare da an sanya batun tsagaita wuta a Lebanon ba.

A nasa bangare shugaba Trump ya ce ya tattaunawa da wakilan Isra’ila da na ƙungiyar Hezbollah kuma sun tabbatar masa da ba za su sake kaiwa juna hari ba.

Da yammacin wannan talatar ake saran wakilan Isra’ila da na Lebanon  za su koma teburin tattaunawa karkashin jagorancin Amurka  da zummar tsawaita yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da mayakan HezbollAh.

Post a Comment

Previous Post Next Post