Amurka ta ware dala miliyan 3.5 don bincike kan take ƴancin addini a Najeriya

Gwamnatin Amurka ta sanar da ware dala miliyan 3 da dubu 500 domin ƙaddamar da shirin sanya idanu da kuma tattara bayanai game da batutuwan take ƴancin gudanar da addini a Najeriya.

Ofishin Ma’aikatar harkokin wajen Amurka da ke kula da batutuwan da suka shafi addini ne ya sanar da ware kuɗaɗen don tallafawa wasu ƙungiyoyi wajen tattara bayanai kan ayyukan take ƴancin gudanar da addini da Washington ke zargin ana yi a Najeriya.

A cewar ma’aikatar, za a shafe tsawon watanni 24 zuwa 48 ana gudanar da aikin, inda Amurka za ta bai wa ƙungiyar kuɗaɗen a matsayin tallafi ko kuma yarjejeniyar aiki na haɗin gwiwa.

Shirin zai mayar da hankali, wajen sanya ido, da tattara bayanai ta hanyar zaƙulo rahotannin da suka shafi take ƴancin addini da mahukuntan Najeriya ko kuma wasu ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi su ka yi.

Ofishin kula da ƴancin gudanar da addini na ƙasa da ƙasa ya buɗe dama ga ƙungiyoyi da ke sha’awar yin wannan muhimman aiki da su miƙa buƙatar hakan ga Amurka.

Amurka ta ce ta samu rahotanni daga ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin addini da ƴan jarida da masana da kuma al’ummomin yankuna da dama, wanda ke tabbatar da cewa ana take ƴancin gudanar da addini a Najeriya, musamman ma ga mabiya addinin Kirista.

Post a Comment

Previous Post Next Post