Farfesa Gwarzo Ya Cika Alƙawarinsa Yayin da MAAUN Ta Miƙa Motar Aiki Ga Jami'ar Northwest Kano

Wata tawaga daga Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) ta miƙa motar aiki kirar Toyota Hilux da wanda ya kafa jami'ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayar ga ofishin Shugabar Jami'ar Northwest Kano (NWUK), Farfesa Amina Salihi Bayero.

Tawagar, wadda Shugaban MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr ya jagoranta, ta haɗa da Mataimakin Shugaban Jami'ar mai kula da harkokin gudanarwa, Dr. Habib Awais Abubakar; memba a Majalisar Dattawan Jami'ar, Dr. Nura Yaro; da Hayatuddeen M. Abdallah daga Sashen Hulɗa da Jama'a na jami'ar.

An tarbi tawagar cikin girmamawa daga Shugabar Jami'ar Northwest Kano tare da manyan jami'an gudanarwar jami'ar.

Miƙa motar ya kasance cika alƙawarin da Farfesa Gwarzo ya yi ne a lokacin wata ziyarar girmamawa da shugabannin NWUK suka kai masa a Abuja, inda ya yi alƙawarin bayar da motar aiki ga ofishin Shugabar jami'ar.

Yayin da yake miƙa motar a madadin wanda ya kafa jami'ar, Shugaban MAAUN ya bayyana cewa wannan tallafi na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami'o'in biyu tare da inganta ayyukan gudanarwa.

Ya kuma sake jaddada ƙudirin Farfesa Gwarzo na ci gaba da tallafa wa ilimi mai zurfi ta hanyar haɗin gwiwa da dabarun bunƙasa harkokin ilimi.

A nata jawabin bayan karɓar motar, Farfesa Amina Salihi Bayero ta gode wa Farfesa Gwarzo bisa cika alƙawarinsa, tana mai bayyana kyautar a matsayin wata sabuwar shaida ta karamcinsa da jajircewarsa wajen bunƙasa ilimi.

Ta tunatar da cewa a baya ma Farfesa Gwarzo ya bai wa jami'ar motar bas mai ɗaukar fasinjoji tare da sauran nau'o'in tallafi.

Har ila yau, ta bayyana cewa Farfesa Gwarzo ya yi alƙawarin taimaka wa NWUK wajen samun tallafin bincike na ƙasa da ƙasa da sauran damammakin da za su inganta bincike, koyarwa da ci gaban jami'ar.

Shi ma Magatakardar Jami'ar NWUK ya bayyana cewa wannan ziyara ta buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin jami'o'in biyu, ciki har da yiwuwar kafa cibiyar haɗin gwiwa ta ilimi da bincike.

Ya yi addu'ar Allah Ya ci gaba da yi wa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo albarka da daukacin ma'aikatan jami'ar MAAUN, yayin da shugaban ɓangaren kuɗi na jami'ar ya bayyana cewa motar za ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta ayyukan gudanarwar jami'ar.

Post a Comment

Previous Post Next Post