Wakilai daga sama da ƙasashe 90, tare da shugabannin addinai, malamai da fitattun mutane daga sassa daban-daban na duniya, sun bayyana shirinsu na halartar jana'izar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da ya yi shahada, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a cewar wani babban jami'in gwamnatin Iran.
Da yake magana a wani taron manema labarai ranar Talata, Mataimakin Ministan Harkokin Cikin Gida na Iran mai kula da harkokin tsaro, kuma sakataren kwamitin shirya jana'izar, Ali Akbar Pourjamshidian, ya ce sama da ƙasashe 30 sun riga sun gabatar da buƙatu a hukumance domin aika manyan tawagoginsu zuwa wajen jana'izar.
Pourjamshidian ya bayyana cewa an ɗan jinkirta gudanar da jana'izar ne domin samar da isasshen lokaci na shirya babban taron ƙasa da ƙasa da na cikin gida, bisa la'akari da halin da ƙasar ke ciki a baya-bayan nan.
Ya kuma ce, bisa shawarar ofishin marigayi jagoran da kuma umarnin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei, za a gudanar da bukukuwan jana'izar na tsawon kwanaki da dama.
Jami'in ya ƙara da cewa an tsara dukkan shirye-shiryen ne ƙarƙashin kulawar Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Ofishin Jagoran Juyin Juya Hali, da kuma wani babban kwamitin ƙasa da gwamnatin Mataimakin Shugaban Ƙasa na Farko, Mohammad Reza Aref, ta kafa.
An kuma kafa kwamitoci na musamman da za su kula da tsaro, sufuri da kayan aiki, ababen more rayuwa, harkokin al'adu, kafafen yaɗa labarai, jami'o'i da hulɗar ƙasa da ƙasa domin tabbatar da gudanar da jana'izar cikin nasara.
Za a gudanar da jana'izar da bukukuwan bankwana a biranen Tehran, Qom, Mashhad da kuma ƙasar Iraki. Haka kuma, an kafa manyan cibiyoyin gudanarwa a Tehran, Qom da lardin Khorasan Razavi, yayin da aka kafa kwamitocin haɗin gwiwa a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa wa jama'a halartar bukukuwan.
Pourjamshidian ya ce gwamnatin Iraki ta kafa nata kwamitin shirya jana'izar ƙarƙashin jagorancin ofishin Firaministan ƙasar, bayan tattaunawa mai zurfi tsakanin jami'an Iran da Iraki, ciki har da ganawar da Ministan Harkokin Wajen Iran, Sayyid Abbas Araghchi, ya yi da Shugaban Ƙasar Iraki, Firaminista da sauran manyan jami'ai.
Bisa jadawalin da aka fitar, za a kai gawar marigayin zuwa Iraki a ranar 8 ga Yuli, inda ake sa ran za a yi mata tarba a filin jirgin saman Baghdad ko Najaf tare da halartar manyan jami'an gwamnatin Iraki. Daga nan kuma za a gudanar da jerin gwanon jana'iza da bukukuwan tunawa a biranen Najaf da Karbala masu tsarki.
A ranar 9 ga Yuli kuwa, za a gudanar da sallar jana'iza da kuma binne gawar a birnin Mashhad, inda ake sa ran za a binne Jagoran da ya yi shahada tare da iyalansa a kusa da Haramin Imam Ridha (A.S.).
Pourjamshidian ya ce manufar waɗannan bukukuwa ita ce nuna ƙarfin ƙasar Iran, ƙarfafa haɗin kan al'ummar Iran da duniyar Musulunci baki ɗaya, tare da sabunta mubaya'a ga sabon jagoran ƙasar.
Ya ƙara da cewa ana sa ran halartar jama'a daga ƙasashen Musulmi irin su Iraki, Pakistan, Afghanistan da sauran maƙwabtan Iran za ta ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin al'ummar Musulmi.
Har ila yau, ya bayyana cewa gwamnati ta ayyana ranakun hutu domin bai wa jama'a damar halartar jana'izar. An ayyana ranakun 4 da 5 ga Yuli a matsayin hutu a lardin Tehran, ranar 6 ga Yuli a matsayin hutun ƙasa baki ɗaya domin babban jerin gwanon jana'iza a Tehran, ranar 7 ga Yuli hutu a birnin Qom, sannan ranar 9 ga Yuli hutu a lardin Khorasan Razavi.
Ya kuma buƙaci mahalarta taron su fi amfani da motocin sufurin jama'a maimakon motocinsu na kashin kansu. Ya ce jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa (Metro) da motocin bas na gwamnatin birnin Tehran za su yi aiki kyauta, yayin da Metro za ta riƙa aiki na sa'o'i 24 a lokacin bukukuwan. Haka kuma, an tanadi manyan wuraren ajiye motoci a mashigai daban-daban na babban birnin domin masu zuwa da motocinsu.
A ƙarshe, Pourjamshidian ya ce sama da 'yan jarida 300 daga ƙasashen waje sun yi rajista domin ɗaukar rahoton jana'izar. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati ba ta da shirin takaita amfani da intanet a lokacin bukukuwan, tare da kafa cibiyar ba da bayanai ta ƙasa domin taimaka wa mahalarta.
Ya ƙara da cewa an zaɓi wurin binne marigayin a Haramin Imam Ridha (A.S.) ne domin sauƙaƙa wa jama'a damar ziyara ba tare da kawo cikas ga sauran baƙi masu ziyara ba.

Post a Comment