Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada matsayar gwamnatin sa na ƙin shiga tattaunawa ko ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga, yana mai cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da zaman sulhu da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata
hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, wadda aka saurara a Kaduna, inda ya ce
gwamnatinsa na ci gaba da goyon bayan dabarar yaƙi da rashin tsaro ta hanyar
amfani da jami’an tsaro maimakon tattaunawa da masu aikata laifuka.
Dauda Lawal ya ce ba abin yarda ba
ne ga kowane mutum ko ƙungiya ta shiga tsakani wajen ƙulla yarjejeniyar zaman
lafiya da ’yan bindiga, yana mai jaddada cewa duk wanda ke yin hakan yana yi ne
a madadinsa ba tare da wakiltar gwamnatin jihar ba.
A cewarsa, tun daga farkon mulkinsa
gwamnati ta tsaya tsayin daka kan cewa ba za ta yi sulhu da ƙungiyoyin da ke da
alhakin kashe-kashe, garkuwa da mutane da kai hare-hare kan al’ummomi a faɗin
jihar ba.
“Ra’ayin neman sulhu da ’yan bindiga
ba ra’ayina ba ne, kuma ba zai taɓa zama haka ba,” in ji gwamnan, yana mai
jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta yi sassauci da masu aikata laifuka ba.
Gwamnan ya bayyana cewa wasu
rahotannin da ke yawo kan cewa an samu yarjejeniyar sulhu a wasu sassan jihar
ba su samu amincewar gwamnatin Zamfara ba.
Ya ce gwamnatin jihar ba ta da hannu
a irin waɗannan shirye-shirye, kuma ba ta sauya matsayarta kan yadda za a
magance matsalar tsaro ba.
Lawal ya nuna cikakken kwarin gwiwa
kan cewa jami’an tsaro za su iya kawo ƙarshen ayyukan ’yan bindiga, yana mai
cewa babu wata ƙungiyar masu laifi da ta fi ƙarfin gwamnatin Najeriya.
“Gwamnati ta fi ƙarfin kowace
ƙungiyar ’yan bindiga,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ci gaba da gudanar
da hare-haren tsaro tare da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro zai taimaka
wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Gwamnan ya tunatar da cewa an yi
ƙoƙarin yin sulhu da ’yan bindiga a baya, amma hakan bai samar da mafita ba.
A maimakon haka, ya ce irin waɗannan
yarjejeniyoyi sun ƙara wa masu aikata laifukan ƙarfin guiwa tare da ba su damar
ci gaba da ayyukansu.
A cewarsa, dabarar tsaron da ake
aiwatarwa yanzu a Zamfara ta fara nuna sakamako mai kyau, inda wasu yankunan da
a baya suka yi ƙaurin suna wajen hare-haren ’yan bindiga suka fara samun
kwanciyar hankali sakamakon ƙara zafafa ayyukan soji.
Dauda Lawal ya yi kira ga al’ummar
jihar da su ci gaba da nuna haƙuri tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a
yaƙin da ake yi da rashin tsaro.
Ya tabbatar musu da cewa gwamnati ba
za ta yi kasa a gwiwa ba wajen lalata hanyoyin sadarwa da sansanonin masu
aikata laifuka.
Gwamnan ya sake nanata cewa hanya
mafi dacewa ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara ita ce ɗaukar mataki
mai tsauri kan ’yan bindiga, ba ta hanyar shiga tattaunawar sulhu da su ba.

Post a Comment