A Najeriya, ƴan bindiga na ci gaba da ƙaddamar da sabbin hare-hare a sassan ƙasar, na baya-bayan nan su ne na jihohin Kogi da Filato na arewacin Najeriya inda kusan mutum 10 suka rasu, yayin da aka sace gwammai.
Da safiyar ranar Litinin rahotanni suka tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kai hari ƙaramar hukumar Kabba/Bunu, inda suka kashe mutum guda, tare da sace wasu fiye da 30.
A cewar majiyoyi, harin ya faru ne da tsakar daren da ya gabata, lamarin da ya jefa al'ummar yankin Ayegunle Bunu cikin tsoro da fargaba. Kwamishinan ƴan sandan Kogi, Nasiru Kankarofi ya tabbatar wa da manema labarai faruwar harin, ana tsaka da bikin yaye sabbin ƴan sandan sarauniya 565 a hedikwatar ƴan sanda da ke Lokoja.
A gefe guda kuma, wasu ƴan bindigar ne suka kashe aƙalla mutane 8, baya ga wasu 10 da suka jikkata, bayan harin da suka kai ƙauyen Gwon-Ajang da ke yankin Foron na ƙaramar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.
Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da daren jiya Lahadi, inda mahara suka buɗe wuta kan al’ummar ƙauyen da suka taru don bikin murnar zagayowar haihuwa. Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi, abinda ya tilasta musu tserewa daga yankin.
.jpeg)
Post a Comment